[1] Me ya sa ƙasashe suke haɗa baki mutane kuma suke ƙulla shawarwarin banza?
[2] Sarakunan duniya sun ɗauki matsayi masu mulki sun taru gaba ɗaya suna gāba da Ubangiji da kuma Shafaffensa.
[3] Suna cewa, “Bari mu tsittsinke sarƙoƙinsu, mu kuma ’yantar da kamammu daga kangin bautar Allah.”
[4] Mai zama a kursiyi a sama yana dariya; Ubangiji yana musu ba’a.
[5] Sa’an nan ya tsawata musu cikin fushinsa ya kuma razanar da su cikin hasalarsa, yana cewa,
[6] “Na kafa Sarkina a kan kursiyi a kan Sihiyona, dutsena mai tsarki.”
[7] Sarki ya yi shelar umarnin Ubangiji. Ubangiji ya ce mini, “Kai Ɗana ne; yau na zama Mahaifinka.
[8] Ka tambaye ni zan kuwa sa al’ummai su zama gādonka, iyakokin duniya su zama mallakarka.
[9] Za ka yi mulkinsu da sandan ƙarfe; za ka farfashe su kucu-kucu kamar tukunyar laka.”
[10] Saboda haka, ku sarakuna, ku yi wayo; ku shiga hankalinku, ku masu mulkin duniya.
[11] Ku bauta wa Ubangiji da tsoro ku kuma yi farin ciki kuna rawar jiki.
[12] Ku sumbaci Ɗan, don kada yă yi fushi ku hallaka a abubuwan da kuke yi, gama fushinsa zai iya kuna farat ɗaya. Masu farin ciki ne dukan waɗanda suke neman mafaka daga gare shi.