[1] Ubangiji ya amsa maka sa’ad da ka yi kira cikin wahala; bari sunan Allah na Yaƙub yă kiyaye ka.
[2] Bari yă aiko maka da taimako daga wuri mai tsarki yă kuma ba ka gudummawa daga Sihiyona.
[3] Bari yă tuna da dukan sadakokinka yă kuma karɓi hadayunka na ƙonawa. Sela
[4] Bari yă biya maka bukatan ranka yă kuma sa dukan shirye-shiryenka su yi nasara.
[5] Za mu yi sowa ta farin ciki sa’ad da ka yi nasara mu kuma ɗaga tutotinmu a cikin sunan Allahnmu. Bari Ubangiji yă biya maka dukan bukatunka.
[6] Yanzu na san cewa, Ubangiji yakan cece shafaffensa. Yakan amsa masa daga samansa mai tsarki da ikon ceto na hannun damansa.
[7] Waɗansu sun dogara a kekunan yaƙi waɗansu kuma a dawakai, amma mu, mun dogara a cikin sunan Ubangiji Allahnmu.
[8] Za a durƙusar da su, su kuma fāɗi, amma mu za mu tashi mu tsaya daram.
[9] Ya Ubangiji, ka ba da nasara ga sarki! Ka amsa mana sa’ad da muka yi kira!