[1] Ya Ubangiji, sarki yana farin ciki cikin ƙarfinka. Yana farin cikinsa ƙwarai cikin nasarorin da ka ba shi!
[2] Ka biya masa bukatar zuciyarsa ba ka kuwa hana masa roƙon da ya yi da leɓunansa ba. Sela
[3] Ka marabce shi da yalwar albarka ka kuma sa masa rawanin zallan zinariya a kansa.
[4] Ya nemi ka ba shi rai, ka kuwa ba shi, tsawo kwanaki, har abada abadin
[5] Ta wurin nasarorin da ka ba shi, ɗaukakarsa mai girma ce; ka mayar masa ɗaukaka da kuma suna.
[6] Tabbatacce ka ba shi madawwamiyar albarka ka kuma sa shi murna da farin cikin kasancewarka.
[7] Gama sarki ya dogara gare ka Ubangiji ta wurin ƙauna marar ƙarewa ta Mafi Ɗaukaka ba zai jijjigu ba.
[8] Hannunka zai kakkama dukan abokan gābanka; hannunka na dama zai kakkama masu ƙinka.
[9] A lokacin bayyanarka za ka sa su zama kamar wutar matoya. Cikin fushinsa Ubangiji zai haɗiye su, kuma wutarsa za tă cinye su.
[10] Za ka hallaka ’ya’yansu daga duniya, zuriyarsu kuma daga ’yan adam.
[11] Ko da yake suna shirya maka mugunta suna kuma ƙirƙiro mugayen dabaru, ba za su yi nasara ba;
[12] gama za ka sa su juye bayansu sa’ad da ka auna su da bakan da ka ja.
[13] Ka sami ɗaukaka, ya Ubangiji cikin ƙarfinka; za mu rera mu kuma yabi ikonka.