Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 4:37

[1] Ya Allah, wanda nake yabo, kada ka yi shiru,

[2] gama mugaye da masu ruɗu sun buɗe bakunansu a kaina; sun yi magana a kaina da harsunan ƙarya.

[3] Da kalmomin ƙiyayya sun kewaye ni; sun tasar mini ba dalili.

[4] A maimakon ƙauna sun sāka mini da zargi, amma ni mutum ne mai addu’a.

[5] Sun sāka mini alheri da mugunta, ƙauna kuma da ƙiyayya.

[6] Ka naɗa mugun mutum yă yi hamayya da shi; bari mai zargi yă tsaya a hannun damansa.

[7] Sa’ad da aka yi masa shari’a, bari a same shi da laifi, bari kuma addu’o’insa su hukunta shi.

[8] Bari kwanakinsa su zama kaɗan; bari wani yă ɗauki wurinsa na shugabanci.

[9] Bari ’ya’yansa su zama marayu matarsa kuma gwauruwa.

[10] Bari ’ya’yansa su zama masu yawo suna bara; bari a yi ta koransu daga gidajensu da suke kufai.

[11] Bari mai binsa bashi yă ƙwace dukan abin da yake da shi; bari baƙi su washe amfanin aikinsa.

[12] Bari kada kowa yă yi masa alheri ko yă ji tausayin marayunsa.

[13] Bari duk zuriyarsa su mutu, a shafe sunayensu daga tsara mai zuwa.

[14] Bari a tuna da laifin kakanninsa a gaban Ubangiji; bari kada a taɓa shafe zunubin mahaifiyarsa.

[15] Bari zunubansu su kasance a gaban Ubangiji kullum, don yă sa a manta da su daga duniya.

[16] Gama bai taɓa yin tunanin yin alheri ba, amma ya tsananta wa matalauta da mabukata da kuma masu fid da zuciya har suka mutu.

[17] Yana jin daɗin la’antarwa, bari yă dawo a kansa; ba ya son sa albarka, bari kada kowa yă sa masa albarka.

[18] Ya sa la’antarwa kamar rigarsa; ta shiga cikin jikinsa kamar ruwa, cikin ƙasusuwansa kamar mai.

[19] Bari tă zama kamar mayafin da aka ɗaura kewaye da shi, kamar ɗamara da aka ɗaura kewaye da shi har abada.

[20] Bari wannan yă zama sakayyar Ubangiji ga masu zargina, ga waɗanda suke mugayen maganganu a kaina.

[21] Amma kai, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ka yi da ni da kyau saboda sunanka; ta alherin ƙaunarka, ka cece ni.

[22] Gama ni matalauci ne mai bukata kuma, zuciyata kuwa ta yi rauni a cikina.

[23] Na ɓace kamar inuwar yamma; ana kakkaɓe ni kamar fāra.

[24] Gwiwoyina suna mutuwa saboda azumi; jikina ya rame ba kuma ƙarfi.

[25] Na zama abin dariya ga masu zargina; sa’ad da suka gan ni, suka kaɗa kawunansu.

[26] Ka taimake ni, ya Ubangiji Allahna; ka cece ni bisa ga ƙaunarka.

[27] Bari su san cewa hannunka ne, cewa kai ne, ya Ubangiji, ka yi shi.

[28] Za su iya la’anta, amma kai za ka sa albarka; sa’ad da suka tasar za su sha kunya, amma bawanka zai yi farin ciki.

[29] Masu zargina za su sha kunya za a rufe su da kunya kamar mayafi.

[30] Da bakina zan ɗaukaka Ubangiji sosai; cikin babban taro zan yabe shi.

[31] Gama yana tsaya a hannun damar mai bukata, don yă cece ransa daga waɗanda suke hukunta shi.

Zabura — Chapters