[1] Ka tanada sarki da shari’arka ta gaskiya, ya Allah, ɗan sarki da adalcinka.
[2] Zai shari’anta mutanenka da adalci, marasa ƙarfinka da shari’ar gaskiya.
[3] Duwatsu za su kawo wadata ga mutane, tuddai kuma su ba da amfani na adalci.
[4] Zai kāre marasa ƙarfi a cikin mutane yă kuma cece ’ya’yan masu bukata; zai murƙushe masu danniya.
[5] Zai jimre muddin rana tana nan, muddin akwai wata, har dukan zamanai.
[6] Zai zama kamar ruwan sama mai fāɗuwa a filin ciyayin da aka yanka, kamar yayyafi mai ba wa duniya ruwa.
[7] A kwanakinsa adalai za su haɓaka wadata za tă yalwata har sai babu sauran wata.
[8] Zai yi mulki daga teku zuwa teku kuma daga Kogi zuwa iyakar duniya.
[9] Kabilun hamada za su rusuna a gabansa abokan gābansa kuwa za su lashe ƙura.
[10] Sarakunan Tarshish da na bakin kogi masu nisa za su ba da gandu gare shi; sarakunan Sheba da Seba za su ba shi kyautai.
[11] Dukan sarakuna za su rusuna masa kuma dukan al’ummai za su bauta masa.
[12] Gama zai ceci masu bukatan da suka yi kuka, marasa ƙarfin da ba su da mai taimako.
[13] Zai ji tausayin gajiyayyu da masu bukata yă ceci masu bukata daga mutuwa.
[14] Zai kuɓutar da su daga danniya da rikici, gama jininsu yake a gabansa.
[15] Bari yă yi doguwar rayuwa! Bari a ba shi zinariya daga Sheba. Bari mutane su riƙa yin addu’a dominsa su kuma albarkace shi dukan yini.
[16] Bari hatsi yă yalwata a duk fāɗin ƙasar; bari yă cika bisan tuddai. Bari ’ya’yan itatuwansa su haɓaka kamar Lebanon; bari yă bazu kamar ciyayi a gona.
[17] Bari sunansa yă dawwama har abada; bari yă ci gaba muddin rana tana nan. Dukan al’ummai za su sami albarka ta wurinsa, za su kuma ce da shi mai albarka.
[18] Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah, Allah na Isra’ila, wanda shi kaɗai ya aikata abubuwa masu banmamaki.
[19] Yabo ya tabbata ga sunansa mai ɗaukaka har abada; bari dukan duniya ta cika da ɗaukakarsa. Amin kuma Amin.
[20] Wannan ya kammala addu’o’in Dawuda ɗan Yesse.