Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 1:00

[1] Sa’ad da Isra’ila ya fito daga Masar, gidan Yaƙub daga mutane masu baƙon harshe,

[2] Yahuda ya zama wuri mai tsarki na Allah, Isra’ila mallakarsa.

[3] Teku ya kalla ya kuma gudu, Urdun ya juye da baya;

[4] duwatsu suka yi tsalle kamar raguna, tuddai kamar tumaki.

[5] Me ya sa, ya teku, kika gudu, Ya Urdun, ka juya baya,

[6] ku duwatsu, kuka yi tsalle kamar raguna, ku tuddai, kamar tumaki?

[7] Ki yi rawar jiki, ya duniya, a gaban Ubangiji, a gaban Allah na Yaƙub,

[8] wanda ya juye dutse ya zama tafki, dutse mai ƙarfi zuwa maɓulɓulan ruwa.

Zabura — Chapters