[1] Kamar yadda barewa take marmarin ruwan rafuffuka, haka raina yake marmarinka, ya Allah.
[2] Raina yana ƙishin Allah, Allah mai rai. Yaushe zan tafi in sadu da Allah ne?
[3] Hawayena ne sun zama abincina dare da rana, yayinda mutane suke ce da ni dukan yini, “Ina Allahnka ɗin?”
[4] Waɗannan abubuwa ne nakan tuna sa’ad da nake faɗin abin da yake a raina, yadda dā nakan tafi tare da taron jama’a, ina bishe su a jere zuwa gidan Allah, da sowa ta farin ciki da kuma godiya a cikin taron biki.
[5] Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina? Me ya sa ka damu a cikina? Ka dogara ga Allah, gama zai sāke yabe shi, Mai Cetona da kuma Allahna.
[6] Raina yana baƙin ciki a cikina; saboda haka zan tuna da kai daga ƙasar Urdun, a ƙwanƙolin Hermon, daga Dutsen Mizar.
[7] Zurfi kan kira zurfi cikin rurin matsirgar ruwanka; dukan raƙuma da igiyoyi sun sha kaina.
[8] Da rana Ubangiji yakan nuna ƙaunarsa, da dare waƙarsa tana tare da ni, addu’a ga Allah na raina.
[9] Na ce wa Allah Dutsena, “Me ya sa ka manta da ni? Me zai sa in yi ta yawo ina makoki, a danne a hannun abokin gāba?”
[10] Ƙasusuwana suna jin jiki da wahala yayinda maƙiyana suna mini ba’a, suna ce mini dukan yini, “Ina Allahnka ɗin?”
[11] Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina? Me ya sa ka damu a cikina? Ka dogara ga Allah, gama zai sāke yabe shi, Mai Cetona da kuma Allahna.