Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 22:26

[1] Albarka ta tabbata ga waɗanda rayuwarsu ba ta da abin zargi, waɗanda suke tafiya bisa ga dokar Ubangiji.

[2] Albarka ta tabbata ga waɗanda suke kiyaye ƙa’idodinsa suke kuma nemansa da dukan zuciyarsu.

[3] Ba sa yin wani abin da ba daidai ba; suna tafiya a hanyoyinsa.

[4] Ka shimfiɗa farillan da dole a yi biyayya da su.

[5] Kash, da a ce hanyoyina tsayayyu ne a yin biyayya da ƙa’idodinka mana!

[6] Da ba zan sha kunya ba sa’ad da na lura da dukan umarnanka.

[7] Zan yabe ka da zuciya ta gaskiya yayinda nake koyon dokokinka masu adalci.

[8] Zan yi biyayya da ƙa’idodinka; kada ka yashe ni ɗungum. ב Bet

[9] Yaya matashi zai kiyaye hanyarsa da tsabta? Sai ta yin rayuwa bisa ga maganarka.

[10] Na neme ka da dukan zuciyata; kada ka bar ni in kauce daga umarnanka.

[11] Na ɓoye maganarka a cikin zuciyata don kada in yi maka zunubi.

[12] Yabo ya tabbata gare ka, ya Ubangiji; ka koya mini ƙa’idodinka.

[13] Da leɓunana na ba da labarin dukan dokokin da suka fito bakinka.

[14] Na yi farin ciki da bin farillanka yadda mutum yakan yi farin ciki da arziki mai yawa.

[15] Na yi tunani a kan farillanka na kuma lura da hanyoyinka.

[16] Na yi murna a cikin ƙa’idodinka; ba zan ƙyale maganarka ba. ג Gimel

[17] Ka yi alheri ga bawanka, zan kuwa rayu; zan yi biyayya da maganarka.

[18] Ka buɗe idanuna don in iya gani abubuwan banmamaki a cikin dokarka.

[19] Ni baƙo ne a duniya; kada ka ɓoye mini umarnanka.

[20] Zuciyata ta ƙosa saboda marmari don dokokinka koyaushe.

[21] Ka tsawata wa masu fariya, waɗanda suke la’anta waɗanda kuma suka kauce daga umarnanka.

[22] Ka cire mini ba’a da reni, gama ina kiyaye farillanka.

[23] Ko da yake masu mulki sun zauna tare suna ɓata mini suna, bawanka zai yi tunani a kan ƙa’idodinka.

[24] Farillanka ne abin farin cikina; su ne mashawartana. ד Dalet

[25] An kwantar da ni ƙasa cikin ƙura; ka kiyaye raina bisa ga maganarka.

[26] Na ba da labari hanyoyina ka kuma amsa mini; ka koya mini ƙa’idodinka.

[27] Bari in gane koyarwar farillanka; sa’an nan zan yi tunani a kan abubuwan banmamakinka.

[28] Raina ya gaji da baƙin ciki; ka ƙarfafa ni bisa ga maganarka.

[29] Ka kiyaye ni daga hanyoyin ruɗu; ka yi mini alheri ta wurin dokokinka.

[30] Na zaɓi hanyar gaskiya; na sa zuciyata a kan dokokinka.

[31] Na riƙe farillanka kankan, ya Ubangiji; kada ka sa in sha kunya.

[32] Ina gudu a kan hanyar umarnanka, gama ka ’yantar da zuciyata. ה He

[33] Ka koya mini Ya Ubangiji, don in bi ƙa’idodinka; sa’an nan zan kiyaye su har ƙarshe.

[34] Ka ba ni ganewa, zan kuwa kiyaye dokarka in kuma yi biyayya da ita da dukan zuciyata.

[35] Ka bi da ni a hanyar umarnanka, gama a can zan sami farin ciki.

[36] Ka juye zuciyata wajen farillanka ba wajen riba ta sonkai ba.

[37] Ka juye idanuna daga abubuwa marasa amfani; ka kiyaye raina bisa ga maganarka.

[38] Ka cika alkawarinka ga bawanka, saboda a ji tsoronka.

[39] Ka kawar da shan kunyar da nake tsoro, gama dokokinka nagari ne.

[40] Ina marmarin farillanka ƙwarai! Ka kiyaye raina cikin adalcinka. ו Waw

[41] Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zo gare ni, ya Ubangiji, cetonka bisa ga alkawarinka;

[42] sa’an nan zan amsa wa masu cin mutuncina, gama na dogara ga maganarka.

[43] Kada ka ƙwace maganarka daga bakina, gama na sa zuciyata a dokokinka.

[44] Kullayaumi zan yi biyayya da dokokinka, har abada abadin.

[45] Zan yi ta yawo a sake gama na nemi farillanka.

[46] Zan yi maganar farillanka a gaban sarakuna ba kuwa za a kunyata ni ba,

[47] gama ina farin ciki da umarnanka saboda ina ƙaunarsu.

[48] Na ɗaga hannuwana ga umarnanka, waɗanda nake ƙauna, ina kuma tunani a kan ƙa’idodinka. ז Zayin

[49] Tuna da maganarka ga bawanka, gama ka ba ni bege.

[50] Ta’aziyyata cikin wahalata ita ce alkawarinka yana kiyaye raina.

[51] Masu fariya suna yi mini ba’a ba tare da an hana su ba, amma ban rabu da dokar ba.

[52] Na tuna da dokokinka na tun dā, ya Ubangiji, na kuwa sami ta’aziyya a cikinsu.

[53] Fushi ya kama ni saboda mugaye, waɗanda suka keta dokokinka.

[54] Ƙa’idodinka su ne kan waƙata a duk inda na sauka.

[55] Da dare na tuna da sunanka, ya Ubangiji, zan kuwa kiyaye dokarka.

[56] Wannan shi ne na saba yi, ina yin biyayya da farillanka. ח Het

[57] Kai ne rabona, ya Ubangiji; na yi alkawarin in kiyaye maganarka.

[58] Na nemi fuskarka da dukan zuciyata; ka yi mini alheri bisa ga alkawarinka.

[59] Na lura da hanyoyina na kuma mayar da matakaina ga farillanka.

[60] Zan gaggauta ba zan ɓata lokaci ba in yi biyayya da umarnanka.

[61] Ko da yake mugaye sun ɗaura ni da igiyoyi, ba zan manta da dokokinka ba.

[62] Da tsakar dare nakan tashi in gode maka saboda dokokinka masu adalci.

[63] Ni aboki ne ga duk mai tsoronka, ga duk wanda yake bin farillanka.

[64] Duniya ta cika da ƙaunarka, ya Ubangiji; ka koya mini ƙa’idodinka. ט Tet

[65] Ka yi wa bawanka alheri bisa ga maganarka, ya Ubangiji.

[66] Ka koya mini sani da kuma hukunci mai kyau, gama na gaskata a umarnanka.

[67] Kafin in sha wahala na kauce, amma yanzu ina biyayya da maganarka.

[68] Kai nagari ne, kuma abin da kake yi yana da kyau; ka koya mini ƙa’idodinka.

[69] Ko da yake masu fariya sun shafe ni da ƙarairayi, na kiyaye farillanka da dukan zuciyata.

[70] Zukatansu sun yi tauri da kuma marasa tausayi amma ina farin ciki a dokarka.

[71] Ya yi kyau da na sha wahala don in koyi ƙa’idodinka.

[72] Doka daga bakinka ya fi mini daraja fiye da azurfa da zinariya guda dubu. י Yod

[73] Hannuwanka ne suka yi suka kuma siffanta ni; ka ba ni ganewa don in koyi umarnanka.

[74] Bari waɗanda suke tsoronka su yi farin ciki sa’ad da suke gan ni, gama na sa zuciyata a maganarka.

[75] Ya Ubangiji na sani, cewa dokokinka masu adalci ne, kuma cikin aminci ka hore ni.

[76] Bari ƙaunarka marar ƙarewa tă yi mini ta’aziyya, bisa ga alkawarinka ga bawanka.

[77] Bari tausayinka yă zo mini don in rayu, gama dokarka ce farin cikina.

[78] Bari masu girman kai su sha kunya saboda abubuwa marasa kyau da suke yi mini ba dalili; amma zan yi tunani a kan farillanka.

[79] Bari waɗanda suke tsoronka su juya gare ni, waɗanda suka gane da farillanka.

[80] Bari zuciyata ta kasance marar abin zargi wajen ƙa’idodinka, don kada in sha kunya. כ Kaf

[81] Raina ya tafke da marmari don cetonka, amma na sa zuciyata a maganarka.

[82] Idanuna sun gaji, suna jiran alkawarinka; Na ce, “Yaushe za ka ta’azantar da ni?”

[83] Ko da yake ni kamar salkar ruwan inabi ne a cikin hayaƙi, ban manta da ƙa’idodinka ba.

[84] Har yaushe bawanka zai yi ta jira? Yaushe za ka hukunta masu tsananta mini?

[85] Masu girman kai sun haƙa mini rami, sun ƙetare dokarka.

[86] Dukan umarnanka abin dogara ne; ka taimake ni, gama mutane suna tsananta mini ba dalili.

[87] Sun kusa gama da ni a duniya, amma ban bar bin farillanka ba.

[88] Ka kiyaye raina bisa ga ƙaunarka, zan kuwa yi biyayya da farillan bakinka. ל Lamed

[89] Maganarka, ya Ubangiji madawwamiya ce; tana nan daram a cikin sammai.

[90] Amincinka yana cin gaba cikin dukan zamanai; ka kafa duniya ta kuma dawwama.

[91] Dokokinka sun dawwama har yă zuwa yau, gama dukan abubuwa suna maka hidima.

[92] Da ba don dokarka ce farin cikina ba, da na hallaka a cikin azabana.

[93] Ba zan taɓa manta da farillanka ba, gama ta wurinsu ne ka kiyaye raina.

[94] Ka cece ni, gama ni naka ne; na yi ƙoƙarin neman farillanka.

[95] Mugaye suna jira su hallaka ni, amma zan yi ta tunani a kan farillanka.

[96] Ga duk cikakke na ga kāsawa; amma umarnanka ba su da iyaka. מ Mem

[97] Kash, ga yadda nake ƙaunar dokarka! Ina tunani a kanta dukan yini.

[98] Umarnanka suna sa in zama mai hikima fiye da abokan gābana, gama kullum suna tare da ni.

[99] Ina da ganewa sosai fiye da dukan malamaina, gama ina tunani a kan farillanka.

[100] Ina da ganewa fiye da dattawa, gama ina biyayya da farillanka.

[101] Na kiyaye ƙafafuna daga kowace muguwar hanya domin in yi biyayya da maganarka.

[102] Ban rabu da dokokinka ba, gama kai da kanka ne ka koya mini.

[103] Ɗanɗanon maganarka akwai zaki, sun ma fi zuma zaki a bakina!

[104] Na sami ganewa daga farillanka; saboda haka ina ƙin kowace hanyar da ba daidai ba. נ Nun

[105] Maganarka fitila ce ga ƙafafuna haske kuma a kan hanyata.

[106] Na yi rantsuwa na kuma tabbatar da shi, cewa zan bi dokokinka masu adalci.

[107] Na sha wahala sosai; ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga maganarka.

[108] Ka karɓi yabon bakina da nake yi da yardar rai, ya Ubangiji, ka kuwa koya mini dokokinka.

[109] Ko da yake kullum ina riƙe da raina a hannuwana, ba zan manta da dokarka ba.

[110] Mugaye sun kafa mini tarko, amma ban kauce daga farillanka ba.

[111] Farillanka su ne gādona har abada; su ne farin cikin zuciyata.

[112] Zuciyata ta shirya a kan kiyaye ƙa’idodinka har ƙarshe. ס Samek

[113] Na ƙi mutane masu baki biyu, amma ina ƙauna dokarka.

[114] Kai ne mafakata da garkuwata; na sa zuciyata a maganarka.

[115] Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta, don in kiyaye umarnan Allahna!

[116] Ka raya ni bisa ga alkawarinka, zan kuwa rayu; kada ka bari a gwale sa zuciyata.

[117] Ka riƙe ni za a kuma cece ni; kullayaumi zan ɗauka ƙa’idodinka da muhimmanci.

[118] Ka ki dukan waɗanda suka kauce daga ƙa’idodinka, gama yaudararsu banza ne.

[119] Dukan mugayen duniya ka zubar kamar datti; saboda haka nake ƙaunar farillanka.

[120] Naman jikina na rawan jiki don tsoronka; na cika da tsoron dokokinka. ע Ayin

[121] Na aikata abin da yake mai adalci da kuma daidai; kada ka ni a hannun masu danne ni.

[122] Ka tabbatar da lafiyar bawanka; kada ka bar masu girman kai su danne ni.

[123] Idanuna sun gaji, da jiran cetonka, da jiran alkawarinka mai adalci.

[124] Ka yi da bawanka bisa ga ƙaunarka ka kuma koya mini ƙa’idodinka.

[125] Ni bawanka ne, ka ba ni fahimi don in gane farillanka.

[126] Lokaci ya yi da za ka yi wani abu, ya Ubangiji; ana karya dokarka.

[127] Saboda ina ƙaunar umarnanka fiye da zinariya, kai, fiye da zinariya zalla,

[128] saboda kuma ina lura da dukan farillanka da kyau, na ƙi kowace hanyar da ba daidai ba. פ Fe

[129] Farillanka masu banmamaki ne; saboda haka nake yin biyayya da su.

[130] Fassarar maganganunka sukan ba da haske; sukan ba da ganewa ga marar ilimi.

[131] Ina hakkin da bakina a buɗe, ina marmarin umarnanka.

[132] Ka juye wurina ka kuma yi mini jinƙai, yadda kullum ka yi wa waɗanda suke ƙaunar sunanka.

[133] Ka bi da sawuna bisa ga maganarka; kada ka bar zunubi yă mallake ni.

[134] Ka fanshe ni daga mutane masu danniya, don in yi biyayya da farillanka.

[135] Ka sa fuskarka ta haskaka a kan bawanka ka kuma koya mini ƙa’idodinka.

[136] Hawaye suna malalowa daga idanuna kamar rafi, gama ba a biyayya da dokarka. צ Tsade

[137] Mai adalci ne kai, ya Ubangiji, dokokinka kuma daidai ne.

[138] Farillan da ka shimfiɗa masu adalci ne; su kuma abin dogara ne ƙwarai.

[139] Kishina ya cinye ni ɗungum, gama abokan gābana sun yi biris da maganganunka.

[140] An gwada alkawuranka sarai, bawanka kuwa yana ƙaunarsu.

[141] Ko da yake ni ba kome ba ne an kuwa rena ni, ba na manta da farillanka.

[142] Adalcinka dawwammame ne dokar kuma gaskiya ce.

[143] Wahala da damuwa suna a kaina, amma umarnanka su ne farin cikina.

[144] Farillanka daidai ne har abada; ka ba ni ganewa don in rayu. ק Kof

[145] Na yi kira da dukan zuciyata; ka amsa mini, ya Ubangiji, zan kuwa yi biyayya da ƙa’idodinka.

[146] Na yi kira gare ka; ka cece ni zan kuwa kiyaye farillanka.

[147] Na tashi kafin fitowar rana na kuma yi kukan neman taimako; na sa zuciyata a maganarka.

[148] Ban rufe idanuna ba dukan dare, don in yi tunani a kan alkawuranka.

[149] Ka ji muryata bisa ga ƙaunarka; ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga dokokinka.

[150] Waɗanda suke ƙirƙiro mugayen dabaru suna nan kusa, amma suna nesa da dokarka.

[151] Duk da haka kana kusa, ya Ubangiji, kuma dukan umarnanka gaskiya ne.

[152] Tun tuni na koyi daga farillanka cewa ka kafa su su kasance har abada. ר Resh

[153] Ka dubi wahalata ka cece ni, gama ban manta da dokarka ba.

[154] Ka kāre manufata ka kuma fanshe ni, ka cece rai na kamar yadda ka alkawarta!

[155] Ceto yana nesa da mugaye, gama ba sa neman ƙa’idodinka.

[156] Tausayinka da girma yake, ya Ubangiji; ka kiyaye raina bisa ga dokokinka.

[157] Maƙiya masu yawa ne suke tsananta mini, amma ban rabu da farillanka ba.

[158] Na dubi marasa aminci da ƙyama, gama ba sa yin biyayya da maganarka.

[159] Dubi yadda nake ƙaunar farillanka; ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga ƙaunarka.

[160] Dukan maganganunka gaskiya ne; dukan dokokinka masu adalci madawwami ne. ש Sin da Shin

[161] Masu mulki suna tsananta mini ba dalili, amma zuciyata na rawan jiki game da maganarka.

[162] Ina farin ciki da alkawarinka kamar yadda wani kan sami ganima mai girma.

[163] Na ƙi ina kuma ƙyamar ƙarya amma ina ƙaunar dokarka.

[164] Sau bakwai a rana ina yabonka saboda dokokinka masu adalci.

[165] Waɗanda suke ƙaunar dokarka suna da babban salama, kuma babu abin da zai sa su yi tuntuɓe.

[166] Ina jiran cetonka, ya Ubangiji, ina kuma bin umarnanka.

[167] Ina biyayya da farillanka, gama ina ƙaunarsu ƙwarai.

[168] Ina biyayya da farillanka da kuma koyarwarka, gama dukan hanyoyina sanannu ne gare ka. ת Taw

[169] Bari kukata ta zo gare ka, ya Ubangiji; ka ba ni ganewa bisa ga maganarka.

[170] Bari roƙona yă zo gabanka; ka cece ni bisa ga alkawarinka.

[171] Bari leɓunana su cika da yabonka, gama ka koya mini ƙa’idodinka.

[172] Bari harshena yă rera game da maganarka, gama dukan umarnanka masu adalci ne.

[173] Bari hannunka yă kasance a shirye don yă taimake ni, gama na zaɓi farillanka.

[174] Ina marmarin cetonka, ya Ubangiji, dokarka kuwa ita ce farin cikina.

[175] Bari in rayu don in yabe ka, bari kuma dokokinka su raya ni.

[176] Na kauce kamar ɓatacciyar tunkiya. Ka nemi bawanka, gama ban manta da umarnanka ba.

Zabura — Chapters