Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 1:07

[1] Sa’ad da Ubangiji ya dawo da kamammu zuwa Sihiyona, mun kasance kamar mutanen da suka yi mafarki.

[2] Bakunanmu sun cika da dariya, harsunanmu da waƙoƙin farin ciki. Sai ana faɗi a cikin al’ummai, “Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominsu.”

[3] Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominmu, mun kuwa cika da farin ciki.

[4] Ka maido da wadatarmu, ya Ubangiji kamar rafuffuka a Negeb.

[5] Waɗanda suka yi shuka da hawaye za su yi girbi da waƙoƙin farin ciki.

[6] Shi da ya fita yana kuka, riƙe da iri don shuki, zai dawo da waƙoƙin farin ciki, ɗauke da dammuna.

Zabura — Chapters