Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 4:31

[1] Mun ji da kunnuwanmu, ya Allah; kakanninmu sun faɗa mana abin da ka aikata a kwanakinsu, tun dā can.

[2] Da hannunka ka kori al’ummai ka kuma dasa kakanninmu; ka ragargaza mutanen ka kuma sa kakanninmu suka haɓaka.

[3] Ba da takobinsu ba ne suka ci ƙasar, ba kuwa ƙarfin hannunsu ne ya ba su nasara ba; hannun damanka ne, ƙarfin hannunka, da kuma hasken fuskarka, gama ka ƙaunace su.

[4] Kai ne Sarkina da kuma Allahna, wanda ya ba da nasarori wa Yaƙub.

[5] Ta wurinka mun tura abokan gābanmu baya; ta wurin sunanka muka tattake maƙiyanmu.

[6] Ba na dogara ga bakana, takobina ba ya kawo nasara;

[7] amma kana ba mu nasara a kan abokan gābanmu, ka sa abokan gābanmu suka sha kunya.

[8] A cikin Allah muke fariyarmu dukan yini, kuma za mu yabi sunanka har abada. Sela

[9] Amma yanzu ka ƙi mu ka kuma ƙasƙantar da mu; ba ka ƙara fita tare da mayaƙanmu.

[10] Ka sa muka gudu a gaban abokin gāba, kuma abokan gābanmu suka washe mu.

[11] Ka ba da mu a cinye kamar tumaki ka kuma watsar da mu a cikin al’ummai.

[12] Ka sayar da mutanenka a kuɗin da bai taka ƙara ya karye ba babu wata riba daga sayar da su da ka yi.

[13] Ka mai da mu abin dariya ga maƙwabtanmu, abin dariya da reni ga waɗanda suke kewaye da mu.

[14] Ka sa muka zama abin ba’a a cikin al’ummai; mutanen suna kaɗa mana kai.

[15] Dukan yini ina cikin wulaƙanci, fuskata kuma ta rufu da kunya

[16] saboda ba’ar waɗanda suke zagi suke kuma ƙina, saboda abokan gābana, waɗanda suka sha alwashi sai sun yi ramuwa.

[17] Dukan wannan ya faru da mu, ko da yake ba mu manta da kai ba ko mu kasance masu ƙarya ga alkawarinka.

[18] Zukatanmu ba su juya baya; ƙafafunmu ba su kauce daga hanyarka ba.

[19] Amma ka ragargaza mu ka kuma maishe mu abin farautar karnukan jeji ka kuma rufe mu cikin duhu baƙi ƙirin.

[20] Da a ce mun manta da sunan Allahnmu ko mun miƙa hannuwanmu ga baƙin alloli,

[21] da Allah bai gane ba, da yake ya san asiran zuciya?

[22] Duk da haka saboda kai mun fuskanci mutuwa dukan yini; aka ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.

[23] Ka farka, ya Ubangiji! Don me kake barci? Ta da kanka! Kada ka ƙi mu har abada.

[24] Me ya sa ka ɓoye fuskarka ka manta da azabanmu da kuma danniyar da ake mana?

[25] An kai mu ƙasa zuwa ƙura; jikunanmu sun manne da ƙasa.

[26] Ka tashi ka taimake mu; ka cece mu saboda ƙaunarka marar ƙarewa.

Zabura — Chapters