Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 1:30

[1] Ka cece ni, ya Allah ta wurin sunanka; ka nuna ni marar laifi ne ta wurin ƙarfinka.

[2] Ka ji addu’ata, ya Allah; ka saurari maganar bakina.

[3] Baƙi suna kawo mini hari; mutane marasa imani suna neman raina, mutanen da ba sa tsoron Allah. Sela

[4] Tabbatacce Allah ne mai taimakona, Ubangiji shi ne wanda yake riƙe ni.

[5] Bari mugunta ta shaƙe masu magana marar kyau a kaina; cikin amincinka ka hallaka su.

[6] Zan miƙa hadaya ta yardar rai gare ka; zan yabe sunanka, ya Ubangiji, gama yana da kyau.

[7] Gama ya cece ni daga dukan wahalolina, idanuna kuma sun ga an yi nasara a kan maƙiyana.

Zabura — Chapters