Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 5:29

[1] Yabi Ubangiji, ya raina. Ya Ubangiji Allahna, kana da girma ƙwarai; kana saye da daraja da ɗaukaka.

[2] Ubangiji ya naɗe kansa da haske kamar riga ya shimfiɗa sammai kamar tenti

[3] ya kafa ginshiƙan ɗakin samansa a kan ruwaye. Ya maido da gizagizai suka zama keken yaƙinsa yana hawa a kan fikafikan iska.

[4] Ya mai da iska suka zama ’yan saƙonsa harsunan wuta kuma bayinsa.

[5] Ya kafa duniya a kan tussanta; ba za a iya matsar da ita ba.

[6] Ka rufe ta da zurfi kamar da riga ruwaye sun tsaya a bisa duwatsu.

[7] Amma a tsawatawarka ruwaye suka gudu da jin ƙarar tsawanka suka ruga da gudu;

[8] suka gudu a bisa duwatsu, suka gangara zuwa cikin kwaruruka, zuwa wurin da ka shirya musu.

[9] Ka kafa iyakar da ba a iya tsallakawa; ba za su ƙara rufe duniya ba.

[10] Ya sa maɓulɓulai suka zuba ruwa cikin kwaruruka; yana gudu tsakanin duwatsu.

[11] Suna ba da ruwa ga dukan namun jeji; jakunan jeji suna kashe ƙishirwansu.

[12] Tsuntsaye sarari suna sheƙunansu kusa da ruwan; suna rera cikin rassa.

[13] Yana wa duwatsu banruwa daga ɗakinsa na sama; ƙasa tana ƙoshiya da amfanin aikinsa.

[14] Yana sa ciyawa tă yi girma saboda shanu, tsire-tsire domin mutum ya nome, suna fid da abinci daga ƙasa,

[15] ruwan inabi yakan sa zuciyar mutum tă yi murna, mai kuwa yakan sa fuska tă yi haske, abinci kuma da yake riƙe zuciyarsa.

[16] Ana yi wa itatuwan Ubangiji banruwa sosai, al’ul na Lebanon da ya shuka.

[17] A can tsuntsaye suke sheƙunnansu; shamuwa tana da gidanta a itatuwan fir.

[18] Manyan duwatsu na awakin jeji ne; tsagaggun duwatsun mafaka ne ga rema.

[19] Wata ne ke ƙididdigar lokuta, rana kuma ta san sa’ad da za tă fāɗi.

[20] Ka yi duhu, sai ya zama dare, sai dukan namun jeji a kurmi suka fito a maƙe.

[21] Zakoki sun yi ruri sa’ad da suke farauta suna kuma neman abincinsu daga Allah.

[22] Rana ta fito, sai suka koma shiru; suka koma suka kwanta a kogwanninsu.

[23] Mutum yakan tafi aikinsa, zuwa wurin aikinsa har yamma.

[24] Ina misalin yawan aikinka, ya Ubangiji! Cikin hikima ka yi su duka; duniya ta cika da halittunka.

[25] Akwai teku, babba da kuma fāɗi, cike da halittun da suka wuce ƙirga, abubuwa masu rai babba da ƙarami.

[26] A can jiragen ruwa suna kai komo, kuma dodon ruwan da ka yi, yă yi wasa a can.

[27] Waɗannan duka suna dogara gare ka don ka ba su abincinsu a daidai lokaci.

[28] Sa’ad da ba su da shi, sai su tattara shi; sa’ad da ka buɗe hannunka, sukan ƙoshi da abubuwa masu kyau.

[29] Sa’ad da ka ɓoye fuskarka, sai su razana; sa’ad da ka ɗauke numfashinsu, sai su mutu su kuma koma ga ƙura.

[30] Sa’ad da ka aika da Ruhunka, sai su halittu, su kuma sabunta fuskar duniya.

[31] Bari ɗaukakar Ubangiji ta dawwama har abada; bari Ubangiji yă yi farin ciki cikin aikinsa,

[32] shi wanda ya dubi duniya, sai ta razana, wanda ya taɓa duwatsu, sai suka yi hayaƙi.

[33] Zan rera ga Ubangiji dukan raina; zan rera yabo ga Allahna muddin ina raye.

[34] Bari tunanina yă gamshe shi, yayinda nake farin ciki a cikin Ubangiji.

[35] Amma bari masu zunubi su ɓace daga duniya mugaye kuma kada a ƙara ganinsu. Yabi Ubangiji, ya raina. Yabi Ubangiji.

Zabura — Chapters