[1] Bari Allah yă tashi, bari a watsar da abokan gābansa; bari maƙiyansa su gudu a gabansa.
[2] Kamar yadda iska take hura hayaƙi, bari yă hura su haka; kamar yadda kaki kan narke a gaban wuta, bari mugaye su hallaka a gaban Allah.
[3] Amma bari adalai su yi murna su kuma yi farin ciki a gaban Allah; bari su yi murna da farin ciki.
[4] Rera wa Allah, rera yabo ga sunansa, ku ɗaukaka wanda yake hawa a kan gizagizai; sunansa Ubangiji ne, ku kuma yi farin ciki a gabansa.
[5] Uba ga marayu, mai kāre gwauraye, shi ne Allah a mazauninsa mai tsarki.
[6] Allah ya shirya masu kaɗaici a cikin iyalai, ya jagorance ’yan kurkuku da waƙoƙi; amma ’yan tawaye suna zama a ƙasa mai zafin rana.
[7] Sa’ad da ka fito a gaban mutanenka, ya Allah, sa’ad da ka taka ta cikin ƙasar da take wofi, Sela
[8] duniya ta girgiza, sammai suka zuba ruwan sama, a gaban Allah, wanda ya bayyana a Sinai, a gaban Allah, Allah na Isra’ila.
[9] Ka ba da yayyafi a yalwace, ya Allah; ka rayar da gādonka da ya gāji.
[10] Mutanenka suka zauna a cikinsa, kuma daga yalwarka, ya Allah, ka tanada wa matalauta.
[11] Ubangiji ya yi umarni, mutane masu yawa ne suka yi shelarsa,
[12] “Sarakuna da mayaƙa suka gudu a gaggauce; cikin sansani mutane sun raba ganima.
[13] Har yayinda kuke barci a cikin garken tumaki, an dalaye fikafikan kurciya da azurfa, fikafikanta da zinariya mai ƙyalli.”
[14] Sa’ad da Maɗaukaki ya watsar da sarakuna a cikin ƙasa, sai ya zama kamar ƙanƙara ta sauka a kan Zalmon.
[15] Duwatsun Bashan, duwatsu masu alfarma ne; duwatsun Bashan masu wuyar hawa ne.
[16] Don me kuke duba da kishi, ya duwatsu masu wuyan hawa, a kan dutsen da Allah ya zaɓa yă yi mulki, inda Ubangiji kansa zai zauna har abada?
[17] Karusan Allah ninkin dubbai goma ne da kuma dubu dubbai; Ubangiji ya zo daga Sinai ya shiga cikin haikalinsa.
[18] Sa’ad da ka hau bisa, ka bi da kamammu cikin tawagarka; ka karɓi kyautai daga mutane, har ma daga ’yan tawaye, don kai, ya Ubangiji Allah, za ka zauna a can.
[19] Yabo ya tabbata ga Ubangiji, ga Allah Mai Cetonmu, wanda kullum yake ɗaukan nauyinmu. Sela
[20] Allahnmu shi ne Allah wanda yake ceto; daga Ubangiji Mai Iko Duka kuɓuta yake zuwa daga mutuwa.
[21] Tabbatacce Allah zai murƙushe kawunan abokan gābansa, rawanin gashi na waɗanda suke ci gaba cikin zunubansa.
[22] Ubangiji ya ce, “Zan kawo su daga Bashan; zan kawo su daga zurfafan teku,
[23] don ku wanke ƙafafunku a cikin jinin maƙiyanku, yayinda harsunan karnukanku su sami rabonsu.”
[24] Jerin gwanonka ya zo a bayyane, ya Allah, jerin gwanon Allahna da Sarkina zuwa cikin wuri mai tsarki.
[25] A gaba akwai mawaƙa, a bayansu akwai makaɗa; tare da su akwai ’yan mata suna bugan ganguna.
[26] Ku yabi Allah cikin taro mai girma; yabi Ubangiji cikin taron Isra’ila.
[27] Ga ƙaramar kabilar Benyamin, suna jagorance su, ga babbar ƙungiya shugabannin Yahuda, ga kuma shugabannin Zebulun da na Naftali.
[28] Ka bayyana ikonka, ya Allah; ka nuna ƙarfinka, ya Allah, kamar yadda ka yi a dā.
[29] Saboda haikalinka a Urushalima sarakuna za su kawo maka kyautai.
[30] Ka tsawata wa naman jejin nan a cikin kyauro, garken bijimai a cikin ’yan maruƙan al’ummai. Ka ƙasƙantar, bari yă kawo sandunan azurfa. Ka watsar da al’ummai waɗanda suke jin daɗin yaƙi.
[31] Jakadu za su zo daga Masar; Kush za tă miƙa kanta ga Allah.
[32] Ku rera wa Allah, ya masarautan duniya, ku rera yabo ga Ubangiji, Sela
[33] gare shi wanda yake hawan daɗaɗɗen sararin sama, wanda yake tsawa da babbar murya.
[34] Ku yi shelar ikon Allah, wanda ɗaukakarsa take a bisa Isra’ila, wanda ikonsa yake a cikin sarari.
[35] Kai mai banmamaki ne, ya Allah, cikin wurinka mai tsarki; Allah na Isra’ila yakan ba da iko da kuma ƙarfi ga mutanensa. Yabo ya tabbata ga Allah!