Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 5:43

[1] Sai Ayuba ya amsa,

[2] “Lalle, na san wannan gaskiya ne. Amma ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah?

[3] Ko da mutum yana so yă yi gardama da shi, ba zai taɓa amsa masa ba ko da sau ɗaya cikin dubu.

[4] Hikimarsa tana da zurfi, ikonsa yana da yawa. Wane ne ya taɓa yin faɗa da shi har ya yi nasara?

[5] Yana matsar da manyan duwatsu kafin su sani kuma yana juya su cikin fushinsa.

[6] Yana girgiza ƙasa, yana girgiza harsashenta.

[7] Yana magana da rana sai ta ƙi yin haske; yana hana taurari yin haske.

[8] Shi kaɗai ya shimfiɗa sammai ya kuma yi tafiya a kan raƙuman ruwan teku.

[9] Shi ne ya halicci Mafarauci da Kare da Zomo, da Kaza, da ’Ya’yanta da tarin taurari a sama, da taurarin kudu.

[10] Yana yin abubuwan banmamaki waɗanda ba a iya ganewa, mu’ujizai waɗanda ba a iya ƙirgawa.

[11] Ba na iya ganinsa lokacin da ya wuce ni; ba na sani ya wuce lokacin da ya wuce.

[12] Wane ne ya isa yă hana shi in ya ƙwace abu? Wa zai ce masa, ‘Me kake yi?’

[13] Allah ba ya danne fushinsa; ko dodannin ruwan da ake kira ayarin Rahab ya tattake su.

[14] “Ta yaya zan iya yin faɗa da shi? Ina zan iya samun kalmomin da zan yi gardama da shi?

[15] Ko da yake ba ni da laifi, ba zan iya amsa masa ba; sai dai roƙon jinƙai zan iya yi ga mahukuncina.

[16] Ko da na yi kira gare shi ya amsa mini, ban yarda cewa zai saurare ni ba.

[17] Zai sa hadari yă danne ni yă ƙara mini ciwona ba dalili.

[18] Ba zai bari in yi numfashi ba, sai dai yă ƙara mini azaba.

[19] In maganar ƙarfi ne, shi babban mai ƙarfi ne! In kuma maganar shari’a ne, wa zai kai kararsa?

[20] Ko da ni marar ƙarfi ne, bakina ya isa yă sa in zama mai laifi; in ba ni da laifi, zai sa in yi laifi.

[21] “Ko da yake ba ni da laifi, ban damu da kaina ba; na rena raina.

[22] Ba bambanci; shi ya sa na ce, ‘Yana hallaka marasa laifi da kuma mugaye.’

[23] Lokacin da bala’i ya kawo ga mutuwa, yakan yi dariyar baƙin cikin marasa laifi.

[24] Lokacin da ƙasa ta faɗa a hannun mugaye, yakan rufe idanun masu shari’a. In ba shi ba wa zai yi wannan?

[25] “Kwanakina sun fi mai gudu wucewa da sauri; suna firiya babu wani abin jin daɗi a cikinsu.

[26] Suna wucewa kamar jirgin ruwan da aka yi da kyauro, kamar jahurma da ta kai wa namanta cafka.

[27] ‘In na ce zan manta da abin da yake damu na, zan yi murmushi in daina nuna ɓacin rai,’

[28] duk da haka ina tsoron duk wahalata, domin na san ba za ka ɗauke ni marar laifi ba.

[29] Tun da an riga an ɗauke ni mai laifi, duk ƙoƙarina a banza yake.

[30] Ko da na wanke jikina duka da sabulu, na wanke hannuwana kuma da soda,

[31] duk da haka za ka jefa ni cikin ƙazamin wuri, yadda ko rigunan jikina ma za su ƙi ni.

[32] “Shi ba mutum ba ne kamar ni wanda zan iya amsa masa, har da za mu yi faɗa da juna a wurin shari’a.

[33] In da akwai wanda zai iya shiga tsakaninmu, ya ɗora hannunsa a kanmu tare,

[34] wani wanda zai sa Allah yă daina duka na, don yă daina ba ni tsoro.

[35] Sa’an nan ne zan iya yin magana ba tare da jin tsoronsa ba, amma a yadda nake a yanzu ba zan iya ba.

Ayuba — Chapters