Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 4:08

[1] Sai Ayuba ya amsa,

[2] “Har yaushe za ku yi ta ba ni azaba ku kuma murƙushe ni da maganganunku?

[3] Yanzu sau goma ke nan kuna wulaƙanta ni, kuna kai mini hari na rashin kunya.

[4] In gaskiya ne na yi laifi, kuskurena ya rage nawa.

[5] In kuwa za ku ɗaukaka kanku a kaina kuna ɗauka wahalar da nake sha domin na yi laifi ne,

[6] sai ku san cewa Allah ya yi mini ba daidai ba ya kewaye ni da ragarsa.

[7] “Ko da yake na yi kuka cewa, ‘An yi mini ba daidai ba!’ Ba a amsa mini ba; ko da yake na nemi taimako, ba a yi adalci ba.

[8] Ya tare mini hanya yadda ba zan iya wucewa ba; ya rufe hanyata da duhu.

[9] Ya cire darajar da nake da ita, ya kuma cire rawani daga kaina.

[10] Ya yi kaca-kaca da ni har sai da na ƙare; ya tuge begen da nake da shi kamar itace.

[11] Yana jin haushina ya lissafta ni cikin maƙiyansa.

[12] Rundunarsa ta zo da ƙarfi; suka kafa sansani kewaye da ni, suka zagaye tentina.

[13] “Ya raba ni da ’yan’uwana maza; abokaina sun zama baƙi gare ni.

[14] Dangina sun tafi; abokaina na kurkusa sun manta da ni.

[15] Waɗanda sukan ziyarce ni, da masu yi mini aiki mata sun ɗauke ni baƙo.

[16] Na kira bawana, amma bai amsa ba, ko da yake na roƙe shi da bakina.

[17] Numfashina yana ɓata wa matata rai; ’yan’uwana sun ƙi ni.

[18] Har ’yan yara suna rena ni; in sun gan ni sai su fara yi mini riyar reni.

[19] Duk abokaina sun yashe ni; waɗanda nake ƙauna sun zama ba sa ƙaunata.

[20] Ni ba kome ba ne sai dai fata da ƙashi, da ƙyar na tsira.

[21] “Ku tausaya mini, abokaina, ku ji tausayina, gama hannun Allah ya sauko a kaina.

[22] Don me kuke fafarata kamar yadda Allah yake yi? Ba ku gaji da yagar fatata ba?

[23] “Kash, da ma a ce ana rubuta maganganuna, da an rubuta su a littafi,

[24] a rubuta su da ƙarfe a kan dutse don su dawwama har abada!

[25] Na san wanda zai fanshe ni yana nan da rai, kuma a ƙarshe zai tsaya a kan duniya.

[26] Kuma bayan an hallaka fatata, duk da haka a cikin jiki zan ga Allah.

[27] Zan gan shi da kaina da idanuna, Ni, ba wani ba ne. Zuciyata ta cika da wannan tunani!

[28] “In kuka ce, ‘Za ku ci gaba da matsa mini, tun da shi ne tushen damuwa,’

[29] sai ku ma ku ji tsoron takobin; gama fushi yakan kawo hukunci ta wurin takobi, sa’an nan za ku san cewa akwai shari’a.”

Ayuba — Chapters