Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:30

[1] Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa,

[2] “Har yaushe za ka gama faɗa waɗannan abubuwa? Maganganunka ba su da amfani.

[3] Allah ba mai shari’ar gaskiya ba ne? Ko Maɗaukaki yakan yi abin da ba daidai ba?

[4] Lokacin da ’ya’yansa suka yi masa zunubi, yakan bar su su sha wahalar da zunubi yake kawowa.

[5] Amma in za ka dubi Allah ka roƙi Maɗaukaki,

[6] in kai mai tsarki ne, kuma mai adalci, ko yanzu ma zai taimake ka, yă mayar maka iyalinka da farin cikinka.

[7] Ko da yake za ka fara da kaɗan, duk da haka za ka gama da samu mai yawa.

[8] “Tambayi na gaba da kai ka ji abin da iyayenka suka koya

[9] gama jiya kaɗai aka haife mu ba mu san kome ba, kuma kwanakinmu a duniya masu wucewa ne.

[10] Ba za su bishe ka su kuma gaya maka abin da za ka yi ba? Ba za su yi magana daga cikin hikimar da suke da ita ba?

[11] Ko kyauro zai iya yi girma a wurin da ba ruwa? Ko za tă taɓa iya yin girma ba tare da ruwa ba?

[12] Yayinda take girma ba a yanka ta, takan mutu da sauri fiye da ciyawa.

[13] Abin da yake faruwa ke nan da duk wanda yake mantawa da Allah; waɗanda ba su da Allah, ba su da bege.

[14] Abin da yake dogara a kai ba shi da ƙarfi; abin da yake dogara a kai yanar gizo ce.

[15] Ya jingina ga yanar gizo, amma ba ta tare shi, sun kama ta, amma ba za tă taimake su tsayawa ba.

[16] Yana kama da shukar da aka ba ta ruwa sosai lokacin da akwai rana sosai, tana yaɗuwa da kyau;

[17] shukar tana bin yaɗuwa, jijiyoyinta suna nannaɗe duwatsu, suna neman wurin da za su kama sosai a cikin duwatsu.

[18] Amma lokacin da aka tuge shukar daga wurin da take, wurin ba zai san da ita kuma ba, wurin zai ce, ‘Ban taɓa ganin ki ba.’

[19] Ba shakka shukar ta mutu ke nan, kuma waɗansu za su tsiro a wurin.

[20] “Ba shakka, Allah ba ya ƙin marar laifi, ko kuma yă ƙarfafa masu aikata mugunta.

[21] Sai dai yă cika bakinka da dariya, yă sa ka yi sowa ta murna.

[22] Maƙiyanka za su sha kunya, za a kawar da tentin mugaye.”

Ayuba — Chapters