Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 4:57

[1] Elihu ya ci gaba,

[2] “Ka ɗan ƙara haƙuri da ni kaɗan, zan kuma nuna maka cewa akwai sauran abubuwan da zan faɗa a madadin Allah.

[3] Daga nesa na sami sanina; zan nuna cewa Mahaliccina shi mai gaskiya ne.

[4] Abin da zan gaya maka ba ƙarya ba ne; mai cikakken sani yana tare da kai.

[5] “Allah mai iko ne, amma ba ya rena mutane; shi mai girma ne cikin manufarsa.

[6] Ba ya barin mugaye da rai sai dai yana ba waɗanda ake tsanantawa hakkinsu.

[7] Ba ya fasa duban masu adalci; yana sa su tare da sarakuna yana ɗaukaka su har abada.

[8] Amma in mutane suna daure da sarƙoƙi, ƙunci kuma ya daure su,

[9] yana gaya musu abin da suka yi, cewa sun yi zunubi da girman kai.

[10] Yana sa su saurari gyara yă kuma umarce su su tuba daga muguntarsu.

[11] In sun yi biyayya suka bauta masa, za su yi rayuwa dukan kwanakinsu cikin wadata shekarunsu kuma cikin kwanciyar zuciya.

[12] Amma in ba su saurara ba, za su hallaka da takobi kuma za su mutu ba ilimi.

[13] “Waɗanda ba su da Allah a zuciyarsu su ne suke riƙe fushi; ko sa’ad da ya ba su horo, ba su neman taimakonsa.

[14] Suna mutuwa tun suna matasa, cikin ƙazamar rayuwar karuwanci.

[15] Amma yana kuɓutar da masu wahala; yana magana da su cikin wahalarsu.

[16] “Yana so yă rinjaye ka daga haƙoran ƙunci, zuwa wuri mai sauƙi inda ba matsi zuwa teburinka cike da abincin da kake so.

[17] Amma yanzu an cika ka da hukuncin da ya kamata a yi wa mugaye; shari’a da kuma gaskiya sun kama ka.

[18] Ka yi hankali kada wani yă ruɗe ka da arziki; kada ka bar toshiya ta sa ka juya.

[19] Dukiyarka ko dukan yawan ƙoƙarinka sun isa su riƙe ka su hana ka shan ƙunci?

[20] Kada ka yi marmari dare yă yi, don a fitar da mutane daga gidajensu.

[21] Ka kula kada ka juya ga mugunta, abin da ka fi so fiye da wahala.

[22] “An ɗaukaka Allah cikin ikonsa. Wane ne malami kamar sa?

[23] Wane ne ya nuna masa hanyar da zai bi, ko kuma wane ne ya ce masa, ‘Ba ka yi daidai ba?’

[24] Ka tuna ka ɗaukaka aikinsa, waɗanda mutane suka yaba a cikin waƙa.

[25] Dukan ’yan adam sun gani; mutane sun hanga daga nesa.

[26] Allah mai girma ne, ya wuce ganewarmu! Yawan shekarunsa ba su bincikuwa.

[27] “Yana sa ruwa yă zama tururi yă zubo daga sama.

[28] Gizagizai suna zubo da raɓarsu kuma ruwan sama yana zubowa ’yan adam a wadace.

[29] Wane ne zai iya gane yadda ya shimfiɗa gizagizai yadda yake tsawa daga wurin zamansa?

[30] Dubi yadda ya baza walƙiyarsa kewaye da shi, tana haskaka zurfin teku.

[31] Haka yake mulkin al’ummai yana kuma tanada abinci a wadace.

[32] Yana cika hannuwansa da walƙiya kuma yana ba ta umarni tă fāɗi a inda ya yi nufi.

[33] Tsawarsa tana nuna cewa babbar iska da ruwa suna zuwa; ko shanu sun san da zuwansa.

Ayuba — Chapters