[1] Ubangiji ya ce wa Ayuba,
[2] “Mai neman sa wa wani laifi zai iya ja da Maɗaukaki? Bari mai tuhumar Allah yă amsa masa.”
[3] Sai Ayuba ya amsa wa Ubangiji,
[4] “Ai, ni ba a bakin kome nake ba ne, ta yaya zan iya amsa maka? Na rufe bakina da hannuna.
[5] Na yi magana sau ɗaya amma ba ni da amsa, sau biyu, amma ba zan ƙara cewa kome ba.”
[6] Sa’an nan Ubangiji ya yi wa Ayuba magana ta cikin guguwa,
[7] “Ka tashi tsaye ka tsaya da ƙarfi kamar namiji; zan yi maka tambaya kuma za ka amsa mini.
[8] “Ko za ka ƙi yarda da shari’ata? Za ka ba ni laifi don ka nuna kai marar laifi ne?
[9] Ko hannunka irin na Allah ne, kuma ko muryarka za tă iya tsawa kamar ta Allah?
[10] Sai ka yi wa kanka ado da ɗaukaka da girma, ka yafa daraja da muƙami.
[11] Ka saki fushinka, ka dubi dukan wani mai girman kai ka wulaƙanta shi.
[12] Ka dubi duk wani mai girman kai ka ƙasƙantar da shi, ka tattake mugaye a inda ka tsaya.
[13] Ka bizne su duka tare ka rufe fuskokinsu a cikin kabari.
[14] Sa’an nan ni kaina zan shaida maka cewa hannun damanka zai iya cetonka.
[15] “Dubi dorina, wadda na halicce ku tare kuma ciyawa take ci kamar sa.
[16] Ga shi ƙarfinta yana a ƙugunta ikonta yana cikin tsokar cikinta.
[17] Wutsiyarta tana da ƙarfi kamar itacen al’ul; jijiyoyin cinyoyinta suna haɗe a wuri ɗaya.
[18] Ƙasusuwanta bututun tagulla ne, haƙarƙarinta kamar sandunan ƙarfe.
[19] Tana ta farko cikin ayyukan Allah, Mahaliccinta kaɗai yake iya tunkarar ta da takobi.
[20] Tuddai su suke tanada mata abinci a inda duk namun jeji suke wasa.
[21] Tana kwanciya a ƙarƙashin inuwar itacen lotus ta ɓuya cikin kyauro da fadama.
[22] Inuwa ta rufe ta da ƙaddaji, itatuwan wardi na rafi, sun kewaye ta.
[23] Sa’ad da kogi ya cika yana hauka, ba tă damu ba; ba abin da zai same ta ko da a gaban bakinta Urdun yake wucewa.
[24] Ko akwai wanda zai iya kama ta ba ta kallo, ko kuma a kama ta da tarko a huda hancinta?