Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 2:37

[1] Sai Elihu ya ce,

[2] “Ko kana tsammani wannan gaskiya ne? Kana cewa, ‘Ni mai adalci ne a gaban Allah.’

[3] Duk da haka kana tambayarsa cewa, ‘Wace riba nake da ita, kuma mene ne zan samu ta wurin ƙin yin zunubi?’

[4] “Zan so in ba ka amsa kai tare da abokanka.

[5] Ku ɗaga kai ku dubi sama ku gani; ku dubi gizagizai a samanku.

[6] In kun yi zunubi ta yaya wannan zai shafi Allah? In zunubanku sun yi yawa, me wannan zai yi masa?

[7] In kuna da adalci, me kuka ba shi, ko kuma me ya karɓa daga hannunku?

[8] Muguntarku takan shafi mutum kamar ku ne kaɗai, adalcinku kuma yakan shafi ’yan adam ne kaɗai.

[9] “Mutane suna kuka don yawan zalunci; suna roƙo don taimako daga hannu mai ƙarfi.

[10] Amma ba wanda ya ce, ‘Ina Allah wanda ya halicce ni, mai ba da waƙoƙi cikin dare,

[11] wanda ya fi koya mana fiye da dabbobin duniya ya kuma sa muka fi tsuntsayen cikin iska hikima.’

[12] Ba ya amsawa lokacin da mutane suka yi kira don taimako domin girman kan mugaye.

[13] Lalle Allah ba ya sauraron roƙonsu na wofi; Maɗaukaki ba ya kula da roƙonsu.

[14] Ta yaya zai saurara sosai ko zai saurara lokacin da kake cewa ba ka ganinsa, cewa ka kawo ƙara a wurinsa kuma dole ka jira shi.

[15] Kuma ka ce, ba ya ba da horo cikin fushinsa ko kaɗan ba ya kula da mugunta.

[16] Saboda haka Ayuba ya buɗe baki yana magana barkatai; yana ta yawan magana ba tare da sani ba.”

Ayuba — Chapters