Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 6:08

[1] Sa’an nan Ubangiji ya amsa wa Ayuba. Ya ce,

[2] “Wane ne wannan da yake ɓata mini shawarata da surutan wofi?

[3] Ka sha ɗamara kamar namiji; zan yi maka tambaya, za ka kuwa amsa mini.

[4] “Kana ina lokacin da na aza harsashen duniya? Gaya mini, in ka sani.

[5] Wane ne ya zāna girmanta? Ba shakka ka sani! Wane ne ya ja layin aunawa a kanta?

[6] A kan me aka kafa tushenta, ko kuma wa ya sa dutsen kan kusurwarta,

[7] yayinda taurarin safe suke waƙa tare dukan mala’iku kuma suka yi sowa don farin ciki.

[8] “Wane ne ya rufe teku a bayan ƙofofi, lokacin da ya burtsatso daga cikin ciki.

[9] Lokacin da na yi wa gizagizai riga na kuma naɗe su a cikin duhu sosai,

[10] sa’ad da na yi masa iyaka na sa masa ƙofofi da wurin kullewa.

[11] Sa’ad da na ce ga iyakar inda za ka kai, ga inda raƙuman ruwanka za su tsaya?

[12] “Ko ka taɓa ba safiya umarni ko kuma ka sa asuba ta fito,

[13] don ta kama gefen duniya ta kakkaɓe mugaye daga cikinta?

[14] Ƙasa ta sāke siffa kamar laka da aka yi wa hatimi; ta fito a fili kamar riga.

[15] An hana mugaye haskensu, hannun da suka ɗaga an karya shi.

[16] “Ko ka taɓa tafiya zuwa maɓulɓulan teku, ko kuma ka taɓa zuwa cikin zurfin lungun teku?

[17] Ko an taɓa nuna maka ƙofar mutuwa? Ko ka taɓa ganin ƙofar inuwar duhun mutuwa?

[18] Ko ka gane fāɗin duniya? Gaya mini, in ka san wannan duka.

[19] “Ina ne hanyar zuwa gidan haske? Kuma a ina duhu yake zama?

[20] Ko za ka iya kai su wurarensu? Ka san hanyar zuwa wurin da suke zama?

[21] Ba shakka ka sani, gama an riga an haife ka a lokacin! Ka yi shekaru da yawa kana rayuwa.

[22] “Ka taɓa shiga rumbunan dusar ƙanƙara ko ka taɓa ganin rumbunan ƙanƙara

[23] waɗanda nake ajiya domin lokacin wahala, domin kwanakin yaƙi da faɗa?

[24] Ina ne hanyar zuwa wurin da ake samun walƙiya, ko kuma inda daga nan ne ake watsa iskar gabas zuwa ko’ina cikin duniya?

[25] Wane ne ya yanka hanyar wucewar ruwa, da kuma hanyar walƙiyar tsawa

[26] don ba da ruwa a ƙasar da ba kowa a wurin jeji inda ba mai zama ciki

[27] don a ƙosar da wurin da ya bushe a sa ciyawa ta tsiro a can?

[28] Ruwan sama yana da mahaifi? Wa ya zama mahaifin raɓa?

[29] Daga cikin wane ne aka haifi ƙanƙara? Wane ne ya haifi jaura daga sammai

[30] lokacin da ruwa ya zama da ƙarfi kamar dutse, lokacin da saman ruwa ya daskare?

[31] “Za ka iya daure kyakkyawar kaza da ’ya’yanta? Ko za ka iya kunce igiyoyin mafarauci da kare da zomo?

[32] Za ka iya tattara taurari bisa ga lokacinsu ko kuma ka bi da beyar da ’ya’yanta zuwa waje?

[33] Ka san dokokin sammai? Ko za ka iya faɗar dangantakar Allah da duniya?

[34] “Za ka iya tsawata wa gizagizai ka kuma rufe kanka da ambaliyar ruwa?

[35] Kai ne kake aika walƙiya da tsawa zuwa inda suke zuwa? Ko suna zuwa wurinka su ce, ‘Ga mu nan mun zo?’

[36] Wane ne yake cika zuciya da hikima ko kuma yake ba zuciya ganewa?

[37] Wane ne yake da hikimar iya ƙirga gizagizai? Wane ne zai iya karkato bakunan tulunan sammai

[38] sa’ad da ƙura ta yi yawa ta daskare a wuri ɗaya?

[39] “Za ka iya farauto wa zakanya nama, ka kuma kawar wa zakoki yunwarsu.

[40] Lokacin da suka kwanta cikin kogunansu, ko kuma lokacin da suke a wurin ɓuyansu?

[41] Wane ne yake ba hankaka abinci lokacin da ’ya’yansa suke kuka ga Allah, kuma suna yawo don rashin abinci?

Ayuba — Chapters