Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 5:02

[1] Sai Elifaz mutumin Teman ya amsa,

[2] “Mutum mai hikima zai amsa da surutai marasa kan gado ko yă cika cikinsa da iskar gabas?

[3] Ko zai yi gardama da maganganun wofi maganganu marasa amfani?

[4] Amma ka ma rena Allah ka hana a yi addu’a gare shi.

[5] Zunubanka ne suke gaya maka abin da za ka ce; kana magana kamar mai wayo.

[6] Bakinka zai kai ka yă baro, ba nawa ba; maganar bakinka za tă juya a kanka.

[7] “Kai ne mutum na farko da aka fara haihuwa? Ko kai ne aka fara halitta kafin tuddai?

[8] Kana sauraron shawarar Allah? Ko kana gani kai kaɗai ne mai hikima?

[9] Me ka sani da ba mu sani ba? Wane fahimi kake da shi da ba mu da shi?

[10] Masu furfura da tsofaffi suna gefenmu mutanen da sun girme babanka.

[11] Ta’aziyyar Allah ba tă ishe ka ba. Maganarsa mai laushi ba tă ishe ka ba?

[12] Don me ka bar zuciyarka ta kwashe ka, kuma don me idanunka suke haske,

[13] har kake fushi da Allah kake kuma faɗar waɗannan maganganu daga bakinka?

[14] “Mene ne mutum, har da zai zama da tsarki, ko kuma mace ta haife shi, har yă iya zama mai adalci?

[15] In Allah bai nuna amincewa ga tsarkakansa ba, in har sammai ba su da tsarki a idonsa,

[16] mutum fa, wanda yake da mugunta da lalacewa, wanda yake shan mugunta kamar ruwa!

[17] “Ka saurare ni, zan kuma yi maka bayani; bari in gaya maka abin da na gani,

[18] abin da masu hikima suka ce, ba tare da sun ɓoye wani abu da suka samu daga wurin iyayensu ba

[19] (waɗanda su ne masu ƙasar kafin baƙi su shigo ƙasar).

[20] Dukan kwanakin ransa mugu yana shan wahala, wahala kaɗai zai yi ta sha.

[21] Ƙara mai bantsoro za tă cika kunnuwansa ’yan fashi za su kai masa hari.

[22] Yana jin tsoron duhu domin za a kashe shi da takobi.

[23] Yana ta yawo, abinci don ungulaye; ya san ranar duhu tana kusa.

[24] Ɓacin rai da baƙin ciki sun cika shi, kamar sarkin da yake shirin yaƙi,

[25] domin ya nuna wa Allah yatsa ya rena Allah Maɗaukaki,

[26] ya tasar masa da faɗa da garkuwa mai kauri da kuma ƙarfi.

[27] “Ko da yake fuskarsa ta cika da kumatu kuma yana da tsoka ko’ina,

[28] zai yi gādon garuruwan da suka lalace, da kuma gidajen da ba wanda yake zama a ciki, gidajen da sun zama tarkace.

[29] Ba zai sāke zama mai arziki ba, dukiyarsa ba za tă dawwama ba, abin da ya mallaka kuma ba zai bazu a ƙasar ba.

[30] Ba zai tsere wa duhu ba; wuta za tă ƙona rassansa, kuma numfashi daga bakin Allah zai hallaka shi.

[31] Kada yă ruɗi kansa ta wurin dogara ga abin da ba shi da amfani domin ba zai samu wani abu ba daga ciki.

[32] Kafin lokacinsa yă cika, za a gama biyansa duka, kuma rassansa ba za su ba da amfani ba.

[33] Zai zama kamar itacen inabi wanda ’ya’yansa suka kakkaɓe kafin su nuna, kamar itacen zaitun zai zubar da furensa.

[34] Gama marasa tsoron Allah za su zama marasa ba da ’ya’ya, wuta kuma za tă ƙona tenti na masu son cin hanci.

[35] Suna yin cikin rikici su kuma haifi mugunta; cikinsu yana cike da ruɗami.”

Ayuba — Chapters