Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:50

[1] Ayuba ya ci gaba da jawabinsa,

[2] “Da ma ina nan lokacin da ya wuce baya can, kwanakin da Allah yake lura da ni,

[3] lokacin da fitilarsa take haske a kaina na yi tafiya cikin duhu tare da haskensa.

[4] Kwanakin da nake tasowa, lokacin da abokantakar Allah ta sa wa gidana albarka,

[5] lokacin da Maɗaukaki yana tare da ni, kuma ’ya’yana suna kewaye da ni,

[6] lokacin da ake zuba madara a inda nake takawa, duwatsu kuma suna ɓulɓulo mini man zaitun.

[7] “Sa’ad da na je ƙofar birni na zauna a bainin jama’a,

[8] matasan da suka gan ni sukan ja gefe tsofaffi kuma suka tashi tsaye;

[9] sarakuna suka yi shiru suka rufe bakunansu da hannuwansu;

[10] Muryar manya ta yi tsit harshensu ya manne a rufin bakunansu.

[11] Duk wanda ya ji ni ya yaba mini waɗanda suka gan ni kuma sun amince da ni,

[12] domin na ceci matalauta waɗanda suka nemi taimako, da marasa mahaifi waɗanda ba su da wanda zai taimake su.

[13] Mutumin da yake bakin mutuwa ya sa mini albarka. Na faranta wa gwauruwa zuciya.

[14] Na yafa adalci ya zama suturata; gaskiya ita ce rigata da rawanina.

[15] Ni ne idon makafi kuma ƙafa ga guragu.

[16] Ni mahaifi ne ga masu bukata; na tsaya wa baƙo.

[17] Na karya ƙarfin mugaye na ƙwato waɗanda suke riƙe da haƙoransu.

[18] “Na yi tunani cewa, ‘Zan mutu a cikin gidana, kwanakina da yawa kamar turɓayar ƙasa.

[19] Jijiyoyina za su kai cikin ruwa, kuma raɓa za tă kwanta a rassana dukan dare.

[20] Ɗaukakata za tă kasance tare da ni garau, bakana koyaushe sabo ne a hannuna.’

[21] “Mutane suna mai da hankali su saurare ni, suna yin shiru don su ji shawarata.

[22] Bayan da na yi magana, ba su ƙara ce kome ba. Maganata ta shige su.

[23] Sukan jira ni kamar yadda ake jiran ruwan sama. Sukan sha daga cikin maganganuna kamar mai shan ruwan bazara.

[24] Sa’ad da na yi musu murmushi da ƙyar sukan yarda; hasken fuskata yana da daraja a gare su.

[25] Na zaɓar masu inda za su bi na kuma zauna kamar sarkinsu; na zauna kamar sarki a cikin rundunansu; ina nan kamar mai yi wa masu makoki ta’aziyya.

Ayuba — Chapters