Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:27

[1] Ayuba kuwa ya ci gaba da magana,

[2] “Na rantse da Allah mai rai, wanda ya danne mini gaskiyata, Maɗaukaki, wanda ya sa nake cikin ɗacin rai.

[3] Muddin ina da rai a cikina kuma numfashin Allah yana cikin hancina,

[4] bakina ba zai faɗi mugun abu ba, harshena kuma ba zai yi ƙarya ba.

[5] Ba zan taɓa yarda cewa kuna da gaskiya ba; har in mutu, ba zan daina kāre mutuncina ba.

[6] Zan ci gaba da adalcina, ba zan fasa ba; lamirina ba zai taɓa yashe ni ba, dukan kwanakin raina.

[7] “Bari maƙiyana su zama kamar mugaye, masu gāba da ni kuma su zama kamar marasa adalci.

[8] Gama wane bege marar tsoron Allah yake da shi, lokacin da aka datse shi, lokacin da Allah ya ɗauke ransa?

[9] Ko Allah yana sauraron kukansa lokacin da ƙunci ya auko masa?

[10] Ko zai sami farin ciki daga Maɗaukaki? Ko zai yi kira ga Allah a kowane lokaci?

[11] “Zan koya muku game da ikon Allah; ba zan ɓoye hanyoyin Maɗaukaki ba.

[12] Duk kun ga wannan ku da kanku saboda haka me ya sa kuke maganganun nan marasa ma’ana?

[13] “Ga abin da mugaye za su samu gādon da azzalumi zai samu daga Maɗaukaki.

[14] Kome yawan ’ya’yansa, takobi za tă gama da su; zuriyarsa ba za su taɓa samun isashen abinci ba.

[15] Waɗanda suka tsira annoba za tă kashe su, kuma gwaurayensu ba za su yi kukan mutuwarsu ba.

[16] Ko da yake ya tara azurfa kamar ƙasa, tufafi kuma kamar tarin ƙasa,

[17] abin da ya tara masu adalci za su sa marasa laifi za su raba azurfarsa.

[18] Gidan da ya gina kamar gidan gizo-gizo, kamar bukkar mai tsaro.

[19] Attajiri zai kwanta, amma daga wannan shi ke nan; lokacin da zai buɗe idanunsa, kome ya tafi.

[20] Tsoro zai kwashe shi kamar ambaliyar ruwa; Da dare iska za tă tafi da shi.

[21] Iskar gabas za tă tafi da shi; shi ke nan ya ƙare; za tă share shi daga wurinsa.

[22] Za tă murɗe shi ba tausayi, lokacin da yake guje wa ikon iskar.

[23] Zai tafa hannu yă yi tsaki yă kawar da shi daga wurinsa.”

Ayuba — Chapters