Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 4:54

[1] Sa’an nan Ayuba ya amsa,

[2] “Da kawai za a iya auna wahalata a kuma sa ɓacin raina a ma’auni!

[3] Ba shakka da sun fi yashin teku nauyi, shi ya sa nake magana haka.

[4] Kibiyoyin Maɗaukaki suna a kaina, ruhuna yana shan dafinsa; fushin Allah ya sauka a kaina.

[5] Jaki yakan yi kuka sa’ad da ya sami ciyawar ci, ko saniya takan yi kuka in ta sami abincinta?

[6] Akan cin abinci marar ɗanɗano ba tare da an sa gishiri ba, ko akwai wani ƙanshin daɗi a cikin farin ruwan ƙwai?

[7] Na ƙi in taɓa shi; irin wannan abinci zai sa ni rashin lafiya.

[8] “Kash, da ma Allah zai ba ni abin da nake fatar samu, da ma Allah zai biya mini bukatata,

[9] wato, Allah yă kashe ni, yă miƙa hannunsa yă yanke raina!

[10] Da sai in ji daɗi duk zafin da nake sha ban hana maganar Mai Tsarkin nan cika ba.

[11] “Wane ƙarfi nake da shi, har da zan ci gaba da sa zuciya? Wane sa zuciya ne zai sa in yi haƙuri?

[12] Da ƙarfin dutse aka yi ni ne? Ko jikina tagulla ne?

[13] Ina da wani ikon da zan iya taimakon kai na ne, yanzu da aka kore nasara daga gare ni?

[14] “Duk wanda ya ƙi yă yi alheri ga aboki ya rabu ta tsoron Maɗaukaki.

[15] Amma ’yan’uwana sun nuna ba zan iya dogara gare su ba, kamar rafin da yakan bushe da rani,

[16] kamar rafin da yakan cika a lokacin ƙanƙara, yă kuma kumbura kamar ƙanƙarar da ta narke,

[17] amma da rani sai yă bushe, lokacin zafi ba a samun ruwa yana gudu a wurin.

[18] Ayari sukan bar hanyarsu; sukan yi ta neman wurin da za su sami ruwa, su kāsa samu har su mutu.

[19] Ayarin Tema sun nemi ruwa, matafiya ’yan kasuwa Sheba sun nema cike da begen samu.

[20] Ransu ya ɓace, domin sun sa zuciya sosai; sa’ad da suka kai wurin kuwa ba su sami abin da suka sa zuciyar samu ba.

[21] Yanzu kuma kun nuna mini ba ku iya taimako; kun ga abin bantsoro kuka tsorata.

[22] Ko na taɓa cewa, ‘Ku ba da wani abu a madadina, ko na roƙe ku, ku ba da wani abu domina daga cikin dukiyarku,

[23] ko kuma kun taɓa kuɓutar da ni daga hannun maƙiyina, ko kun taɓa ƙwato ni daga hannun marasa kirki’?

[24] “Ku koya mini, zan yi shiru; ku nuna mini inda ban yi daidai ba.

[25] Faɗar gaskiya tana da zafi! Amma ina amfanin gardamar da kuke yi?

[26] Ko kuna so ku gyara abin da na faɗi ne, ku mai da magana wanda yake cikin wahala ta zama ta wofi?

[27] Kukan yi ƙuri’a a kan marayu ku kuma sayar da abokinku.

[28] “Amma yanzu ku dube ni da kyau, zan yi muku ƙarya ne?

[29] Ku bi a hankali, kada ku ɗora mini laifi; ku sāke dubawa, gama ba ni da laifi.

[30] Ko akwai wata mugunta a bakina? Bakina ba zai iya rarrabewa tsakanin gaskiya da ƙarya ba?

Ayuba — Chapters