Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 5:05

[1] “Amma yanzu, Ayuba, ka saurari abin da zan ce; ka sa hankali ga kowane abin da zan faɗa.

[2] Zan yi magana; kalmomina suna dab da fitowa daga bakina.

[3] Abin da zan faɗa gaskiya ne daga cikin zuciyata; bakina zai faɗi gaskiyar abin da na sani.

[4] Ruhun Allah ne ya yi ni; numfashin Maɗaukaki ya ba ni rai.

[5] Ka amsa mini in za ka iya; ka yi shirin fuskanta ta.

[6] Ni kamar ka nake a gaban Allah; ni ma daga ƙasa aka yi ni.

[7] Kada ka ji tsorona, ba abin da zai fi ƙarfinka.

[8] “Amma ka faɗa na ji, na ji daidai abin da ka faɗa,

[9] ‘ni mai tsarki ne marar zunubi; ina da tsabta kuma ba ni da laifi.

[10] Duk da haka Allah ya same ni da laifi; ya ɗauke ni maƙiyinsa,

[11] ya daure ƙafafuna da sarƙa; yana tsaron duk inda na bi.’

[12] “Amma na gaya maka, a nan ba ka yi daidai ba, gama Allah ya fi mutum girma.

[13] Don me ka yi masa gunaguni cewa ba ya amsa tambayoyin mutum?

[14] Gama Allah yana magana, yanzu ga wannan hanya, yanzu kuma ga wata hanya ko da yake ba lalle mutum yă lura ba.

[15] A cikin mafarki, cikin wahayi da dare, sa’ad da barci mai zurfi ya fāɗo a kan mutane lokacin da suke cikin barci kan gadajensu,

[16] mai yiwuwa yă yi musu magana a cikin kunnuwansu yă razana su da gargaɗinsa,

[17] don a juyar da su daga abin da yake yi da ba daidai ba a kuma hana su daga girman kai,

[18] don a kāre su daga fāɗuwa cikin rami, a kāre su daga hallaka ta wurin takobi.

[19] “Ko kuma mutum yă sha horo ta wurin kwanciya da ciwo da rashin jin daɗi cikin ƙasusuwansa,

[20] yadda zai ji ƙyamar abinci, har yă ƙi son abinci mafi daɗi.

[21] Naman jikinsa ya lalace ba wani abu mai kyau a ciki kuma ƙasusuwansa da suke a rufe da tsoka yanzu duk sun fito.

[22] Ransa yana matsawa kusa da rami, ransa kuma kusa da ’yan aikan mutuwa.

[23] Duk da haka, in akwai mala’ika a gefensa kamar matsakanci, ɗaya daga cikin dubu, da zai gaya wa mutum abin da yake daidai gare shi,

[24] yă yi masa alheri yă ce, ‘Kada ka bari yă fāɗa cikin rami, na samu fansa dominsa.’

[25] Sa’an nan fatar jikinsa za tă zama sabuwa kamar ta jariri; za tă zama kamar lokacin da yake matashi.

[26] Ya yi addu’a ga Allah ya kuwa samu alheri a wurinsa, yana ganin fuskar Allah yana kuma yin sowa don murna; Allah ya mayar da shi ya zama mai adalci.

[27] Sa’an nan sai ya zo wurin, wurin mutane ya ce, ‘Na yi zunubi, na kauce wa abin da yake daidai, amma ban samu abin da ya kamata in samu ba.

[28] Ya fanshi raina daga fāɗawa cikin rami, kuma zan rayu in ji daɗin hasken.’

[29] “Allah ya yi wa mutum duk waɗannan, sau biyu, har ma sau uku.

[30] Ya juyo da ransa daga fāɗawa cikin rami, don hasken rai ya haskaka a kansa.

[31] “Ka sa hankali da kyau, Ayuba, ka saurare ni; ka yi shiru zan yi magana.

[32] In kana da abin da za ka ce, ka amsa mini; yi magana, domin ina so in ’yantar da kai.

[33] Amma in ba haka ba, sai ka saurare ni; yi shiru, zan kuma koya maka hikima.”

Ayuba — Chapters