Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:34

[1] “Mutum haihuwar mace kwanakinsa kaɗan ne, kuma cike da wahala.

[2] Yana tasowa kamar fure yana kuma shuɗewa; kamar inuwa, ba ya daɗewa.

[3] Za ka zura ido a kan irin wannan ne? Za ka kawo shi gaba don ka yi masa shari’a?

[4] Wane ne zai iya kawo abin da yake da tsarki daga cikin abu marar tsarki? Babu!

[5] An lissafta kwanakin mutum; ka riga ka ɗibar masa watanni, ka yi masa iyaka, ba zai iya wuce iyakar ba.

[6] Saboda haka ka kawar da kanka daga gare shi, ka rabu da shi har sai ya cika lokacinsa kamar mutumin da aka ɗauki hayarsa.

[7] “Aƙalla itace yana da bege. In an sare shi, zai sāke tsira, zai tohu da kyau.

[8] Ko da jijiyoyin itacen sun tsufa a cikin ƙasa kuma kututturensa ya mutu a cikin ƙasa.

[9] Daga ya ji ƙanshin ruwa zai tohu yă yi tsiro kamar shuka.

[10] Amma mutum yana mutuwa a bizne shi; daga ya ja numfashinsa na ƙarshe, shi ke nan.

[11] Kamar yadda ruwa yake bushewa a teku ko a gaɓar rafi sai wurin yă bushe,

[12] haka mutum zai kwanta ba zai tashi ba; har sai duniya ta shuɗe mutane ba za su farka ba, ba za su tashi daga barcinsu ba.

[13] “Da ma za ka ɓoye ni a cikin kabari ka ɓoye ni har sai fushinka ya wuce! In da za ka keɓe mini lokaci sa’an nan ka tuna da ni!

[14] In mutum ya mutu, ko zai sāke rayuwa? In haka ne zan daure kwanakin da nake shan wahala har su wuce.

[15] Za ka kira zan kuwa amsa maka; za ka yi marmarin abin da hannunka ya halitta.

[16] Ba shakka a lokacin ne za ka lura da matakaina amma ba za ka kula da zunubaina ba.

[17] Za a daure laifofina a cikin jaka; za ka rufe zunubaina.

[18] “Amma kamar yadda manyan duwatsu suke fāɗuwa su farfashe su kuma gusa daga wurarensu,

[19] yadda ruwa yakan zaizaye duwatsu ruwa mai ƙarfi kuma yă kwashe turɓayar ƙasa, haka kake barin mutum ba bege.

[20] Ka sha ƙarfinsa gaba ɗaya, sai ya ɓace, ka sauya yanayinsa ka kuma kore shi.

[21] Ko an martaba ’ya’yansa maza, ba zai sani ba; Ko an wulaƙanta su, ba zai gani ba.

[22] Zafin jikinsa kaɗai yake ji yana kuka wa kansa ne kaɗai.”

Ayuba — Chapters