Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:40

[1] Sai mutanen nan uku suka daina amsa wa Ayuba, domin a ganinsa shi mai adalci ne.

[2] Amma Elihu ɗan Barakel mutumin Buz na iyalin Ram, ya ji haushi da Ayuba don yă nuna shi ne mai gaskiya ba Allah ba.

[3] Ya kuma ji haushin abokan nan guda uku, don sun kāsa amsa wa Ayuba ko da yake sun nuna Ayuba ne yake da laifi.

[4] Elihu ya jira sai a wannan lokaci ne ya yi magana da Ayuba, don shi ne yaro a cikinsu duka.

[5] Amma sa’ad da Elihu ya ga mutanen nan uku ba su da abin cewa, sai ya fusata.

[6] Sai Elihu ɗan Barakel mutumin Buz ya ce, “Ni ƙarami ne a shekaru, ku kuma kun girme ni; shi ya sa na ji tsoro na kāsa gaya muku abin da na sani.

[7] Na ɗauka ya kamata ‘shekaru su yi magana; ya kamata yawan shekaru su koyar da hikima.’

[8] Amma ruhun da yake cikin mutum, numfashin Maɗaukaki shi ne yake ba shi ganewa.

[9] Ba tsofaffi ne kaɗai suke da hikima ba, ba masu yawan shekaru ne suke gane abin da yake daidai ba.

[10] “Saboda haka nake ce muku, ku saurare ni; ni ma zan gaya muku abin da na sani.

[11] Na jira sa’ad da kuke magana, na ji muhawwararku lokacin da kuke neman abin da za ku faɗa,

[12] na saurare ku da kyau. Amma ba waninku da ya nuna Ayuba yana da laifi; ba ko ɗayanku da ya amsa muhawwararsa.

[13] Kada ku ce, ‘Mun sami hikima; Allah ne kaɗai yake da ikon yin nasara da shi ba mutum ba.’

[14] Amma ba da ni Ayuba ya yi gardama ba kuma ba zan amsa masa da irin amsarku ba.

[15] “Mamaki ya kama su kuma ba su da abin cewa; kalmomi sun kāsa musu.

[16] Dole ne in jira yanzu da suka yi shiru, yanzu da suke tsaye a wurin ba su da amsa.

[17] Ni ma zan faɗi nawa; ni ma zan faɗi abin da na sani.

[18] Gama ina cike da magana, kuma ruhun da yake cikina yana iza ni;

[19] a ciki ina kamar ruwan inabi wanda aka rufe a cikin kwalaba, kamar sabuwar salkar ruwan inabi mai shirin fashewa.

[20] Dole in yi magana in sami lafiya; dole in buɗe baki in ba da amsa.

[21] Ba zan nuna wa wani sonkai ba, ko kuma in yi wa wani daɗin baki ba;

[22] gama da a ce na iya daɗin baki, da wanda ya yi ni ya ɗauke ni daga nan tuntuni.

Ayuba — Chapters