Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:48

[1] “Idanuna sun ga waɗannan duka, kunnuwana sun ji sun kuma gane.

[2] Abin da kuka sani, ni ma na sani; ba ku fi ni ba.

[3] Amma ina so in yi magana da Maɗaukaki, in kai kukana wurin Allah kai tsaye.

[4] Ku kuma kun ishe ni da ƙarairayi; ku likitocin wofi ne, dukanku!

[5] In da za ku yi shiru gaba ɗaya! Zai zama muku hikima.

[6] Ku ji gardamata yanzu; ku ji roƙon da zai fito daga bakina.

[7] Za ku iya yin muguwar magana a madadin Allah? Ko za ku yi ƙarya a madadinsa?

[8] Ko za ku nuna masa sonkai? Ko za ku yi gardama a madadinsa?

[9] In ya bincike ku zai tarar ba ku da laifi? Ko za ku iya ruɗe shi yadda za ku ruɗi mutane?

[10] Ba shakka zai kwaɓe ku in kun nuna sonkai a ɓoye.

[11] Ko ikonsa ba ya ba ku tsoro? Tsoronsa ba zai auka muku ba?

[12] Duk surutanku kamar toka suke; kāriyarku na yimɓu ne.

[13] “Ku yi shiru zan yi magana; sa’an nan abin da zai same ni yă same ni.

[14] Don me na sa kaina cikin hatsari na yi kasada da raina?

[15] Ko da zai kashe ni ne, begena a cikinsa zai kasance; ba shakka zan kāre kaina a gabansa

[16] lalle wannan zai kawo mini kuɓuta gama ba wani marar tsoron Allah da zai iya zuwa wurinsa!

[17] Ku saurara da kyau ku ji abin da zan faɗa; bari kunnuwanku su ji abin da zan ce.

[18] Yanzu da na shirya ƙarata, na san za a ce ba ni da laifi.

[19] Ko wani zai ce ga laifin da na yi? In an same ni da laifi, zan yi shiru in mutu.

[20] “Kai dai biya mini waɗannan bukatu biyu kawai ya Allah, ba zan kuwa ɓoye daga gare ka ba;

[21] Ka janye hannunka nesa da ni, ka daina ba ni tsoro da bantsoronka.

[22] Sa’an nan ka kira ni, zan kuwa amsa, ko kuma ka bar ni in yi magana sai ka amsa mini.

[23] Abubuwa nawa na yi waɗanda ba daidai ba, kuma zunubi ne? Ka nuna mini laifina da zunubina.

[24] Don me ka ɓoye mini fuskarka; ka kuma sa na zama kamar maƙiyinka?

[25] Ko za a wahalar da ganye wanda iska take hurawa? Ko za ka bi busasshiyar ciyawa?

[26] Gama ka rubuta abubuwa marasa daɗi game da ni; ka sa na yi gādon zunuban ƙuruciyata.

[27] Ka daure ƙafafuna da sarƙa; kana kallon duk inda na taka ta wurin sa shaida a tafin ƙafafuna.

[28] “Haka mutum yake lalacewa kamar ruɓaɓɓen abu, kamar rigar da asu ya cinye.

Ayuba — Chapters