[1] Sai Elifaz mutumin Teman ya amsa,
[2] “Mutum yana iya zama da amfani a wurin Allah? Mai hikima ma zai iya zama da amfani a wurin shi?
[3] Wane daɗi Allah zai ji in kai mai adalci ne? Wace riba zai samu in rayuwarka marar laifi ce?
[4] “Ko don kana tsoron Allah shi ya sa ya kwaɓe ka ya kuma bari haka yă same ka?
[5] Ba muguntarka ce ta yi yawa ba? Ba zunubanka ne ba iyaka ba?
[6] Ka sa ɗan’uwanka yă biya ka bashin da kake binsa ba dalili; ka ƙwace wa mutanen rigunansu ka bar su tsirara.
[7] Ba ka ba masu jin ƙishirwa su sha ba kuma ka hana wa masu jin yunwa abinci su ci.
[8] Ko da yake kai mai ƙarfi ne, ka mallaki ƙasa, mutum mai martaba kuma, kana zama cikin ƙasarka.
[9] Ka kori gwauraye hannu wofi, ka kuma karya ƙarfin marayu.
[10] Shi ya sa kake kewaye da tarkuna, shi ya sa ka cika da tsoron mugun abin da zai auko maka.
[11] An yi duhu ƙwarai, har ba ka iya gani, shi ya sa ambaliyar ruwa ta rufe ka.
[12] “Ba Allah ne a can sama ba? Dubi yadda taurarin sama suke can nesa a sama!
[13] Duk da haka ka ce, ‘Me Allah ya sani? A cikin duhu ne yake shari’a?
[14] Gajimare ya rufe shi, saboda haka ba ya ganinmu lokacin da yake takawa a cikin sammai.’
[15] Za ka ci gaba da bin tsohuwar hanyar da mugayen mutane suka bi?
[16] An ɗauke su kafin lokacinsu yă cika, ruwa ya share tushensu.
[17] Suka ce wa Allah, ‘Ka rabu da mu! Me Maɗaukaki zai yi mana?’
[18] Duk da haka kuwa shi ne ya cika gidajensu da abubuwa masu kyau, saboda haka ba ruwana da shawarar mugaye.
[19] “Masu adalci suna gani ana hallaka mugaye, suna jin daɗi; marasa laifi suna yi musu ba’a, suna cewa,
[20] ‘Ba shakka an hallaka maƙiyanmu, wuta kuma ta ƙona dukiyarsu.’
[21] “Ka miƙa kanka ga Allah ka samu salamarsa; ta haka ne arziki zai zo maka.
[22] Ka bi umarnin da zai fito daga bakinsa kuma ka riƙe maganarsa a cikin zuciyarka.
[23] In ka komo ga Maɗaukaki, za ka warke. In ka kawar da mugunta daga cikin gidanka.
[24] Ka jefar da zinariyarka a ƙasa, ka jefar da zinariyar Ofir da ka fi so a cikin duwatsu,
[25] sa’an nan ne Maɗaukaki zai zama zinariyarka, zai zama azurfa mafi kyau a wurinka.
[26] Ba shakka a lokacin ne za ka sami farin ciki daga wurin Maɗaukaki, ku kuma ɗaga idanunku ga Allah
[27] Za ka yi addu’a zuwa gare shi, zai kuwa ji ka, kuma za ka cika alkawuranka.
[28] Abin da ka zaɓa za ka yi za ka yi nasara a ciki, haske kuma zai haskaka hanyarka.
[29] Sa’ad da aka ƙasƙantar da mutane ka kuma ce, ‘A ɗaga su!’ Sa’an nan zai ceci masu tawali’u.
[30] Zai ceci wanda ma yake mai laifi, wanda zai tsirar da shi ta wurin tsabtar hannuwanka.”