Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 5:39

[1] Sa’an nan Elihu ya ce,

[2] “Ku ji maganata, ku masu hikima; ku saurare ni, ku masu ilimi.

[3] Gama kunne yana rarrabe magana kamar yadda harshe yake ɗanɗana abinci.

[4] Bari mu zaɓi abin da yake daidai, bari mu koyi abin da yake mai kyau tare.

[5] “Ayuba ya ce, ‘Ba ni da laifi, amma Allah ya hana mini hakkina.

[6] Ko da yake ina da gaskiya, an ɗauke ni maƙaryaci; ko da yake ba ni da laifi, kibiyoyinsa sun ji mini ciwo wanda ba ya warkewa.’

[7] Wane mutum ne kamar Ayuba, wanda yake shan ba’a kamar ruwa?

[8] Yana abokantaka da masu aikata mugunta; yana cuɗanya da mugaye.

[9] Gama ya ce, ‘Ba ribar da mutum zai samu lokacin da yake ƙoƙari yă faranta wa Allah zuciya.’

[10] “Saboda haka ku saurare ni, ku masu ganewa. Ko kaɗan Allah ba ya mugunta, Maɗaukaki ba ya kuskure.

[11] Yana biyan mutum bisa ga abin da ya yi; yana kawo masa abin da ayyukansa suka jawo.

[12] Ba zai yiwu Allah yă yi ba daidai ba, Maɗaukaki ba zai yi shari’a marar gaskiya ba.

[13] Wane ne ya ba shi iko yă lura da duniya? Wane ne ya ba shi iko kan dukan duniya?

[14] In nufinsa ne ya kuma janye ruhunsa da numfashinsa,

[15] ’yan adam duka za su hallaka tare, mutum kuma zai koma ƙasa.

[16] “In kana da ganewa sai ka saurari wannan; ka saurari abin da zan ce.

[17] Maƙiyin gaskiya zai iya yin mulki? Za ka iya ba mai gaskiya, Maɗaukaki laifi?

[18] Ba shi ne ya ce wa sarakuna, ‘Ba ku da amfani ba,’ ya ce wa manya ‘Ku mugaye ne,’

[19] wanda ba ya nuna sonkai ga ’ya’yan sarki kuma ba ya goyon bayan masu arziki a kan matalauta, gama dukansu shi ya yi su da hannuwansa.

[20] Suna mutuwa nan take, a cikin tsakiyar dare; an girgiza mutanen amma sun wuce; an taɓa manya amma ba da hannun mutum ba.

[21] “Idanunsa suna kan al’amuran mutane; yana ganin tafiyarsu duka.

[22] Babu wuri mai duhu, babu inuwa mai duhu, inda masu aikata mugunta za su ɓoye.

[23] Allah ba ya bukata yă ci gaba da bincike mutane, har da za su zo gabansa don yă shari’anta su.

[24] Ba tare da tambaya ba yana ragargaza masu iko, yă kuma sa waɗansu a wurinsu.

[25] Gama yana sane da abubuwan da suke yi, yana hamɓarar da su da dare a kuma ragargaza su.

[26] Yana ba su horo, don muguntarsu, inda kowa zai gan su,

[27] domin sun juya daga binsa, kuma ba su kula da hanyoyinsa ba.

[28] Sun sa kukan matalauta ya kai wurinsa yadda ya kai ga jin kukan masu bukata.

[29] Amma in ya yi shiru, wa zai ba shi laifi? In ya ɓoye fuskarsa, wa zai gan shi? Duk da haka shi yake da iko kan mutum da al’umma duka,

[30] yana hana wanda bai san Allah ba yă yi mulki, ya hana shi sa wa mutane tarko.

[31] “A ce mutum ya ce wa Allah, ‘Na yi laifi, amma ba zan sāke saɓa wa wani ba.

[32] Ka koya mini abin da ba zan iya gani ba; in na yi ba daidai ba, ba zan sāke yi ba.’

[33] Ya kamata Allah yă yi maka bisa ga abin da ka ce ne, sa’ad da ka ƙi ka tuba? Dole kai ka zaɓa, ba ni ba; yanzu ka gaya mini abin da ka sani.

[34] “Mutane masu ganewa za su ce, masu hikima waɗanda suka ji ni za su ce mini,

[35] ‘Ayuba ya yi magana cikin rashin sani; maganganunsa na marar hikima ne.’

[36] Kash, da za a gwada Ayuba har ƙarshe, domin yana ba da amsa kamar mugun mutum.

[37] Ya ƙara tawaye a kan zunubansa; ya tafa hannuwansa na reni a cikinmu ya kuma ƙara yawan maganganunsa ga Allah.”

Ayuba — Chapters