Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:13

[1] Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa,

[2] “Yaushe za ka gama maganganun nan? Ka dawo da hankalinka sa’an nan za mu iya yin magana.

[3] Don me muke kamar shanu a wurinka, ka ɗauke mu mutanen wofi?

[4] Kai da ka yayyage kanka don haushi, za a yashe duniya saboda kai ne? Ko kuma duwatsu za su matsa daga wurinsu?

[5] “An kashe fitilar mugu; harshen wutarsa ya daina ci.

[6] Wutar cikin tentinsa ta zama duhu; fitilar da take kusa da shi ta mutu.

[7] Ƙarfin takawarsa ya ragu; dabararsa ta ja fāɗuwarsa.

[8] Ƙafafunsa sun kai shi cikin raga, yana ta yawo a cikin ragar.

[9] Tarko ya kama ɗiɗɗigensa; tarko ya riƙe shi kam.

[10] An ɓoye masa igiya da za tă zarge shi a ƙasa; an sa masa tarko a kan hanyar da zai bi.

[11] Tsoro duk ya kewaye shi ta kowane gefe yana bin shi duk inda ya je.

[12] Masifa tana jiransa; bala’i yana shirye yă fāɗa masa a lokacin da zai fāɗi.

[13] Ya cinye wani sashe na gaɓar jikinsa; ɗan fari na mutuwa ya cinye ƙafafunsa.

[14] An yage shi daga zaman lafiyar da yake yi a cikin tentinsa aka sa shi tsoro sosai.

[15] Wuta ta cinye tentinsa; farar wuta ta rufe wurin da yake zama.

[16] Jijiyoyinsa sun bushe a ƙasa rassansa sun mutu a sama.

[17] An manta da shi a duniya; ba wanda yake ƙara tunawa da shi.

[18] An tura shi daga cikin haske zuwa cikin duhu, an kore shi daga duniya.

[19] Ba shi da ’ya’ya ko zuriya cikin mutanensa, ba sauran wanda yake a raye a wurin da ya taɓa zama.

[20] Mutanen Yamma suna mamakin abin da ya faru da shi; tsoro ya kama mutanen gabas.

[21] Ba shakka haka wurin zaman mugun mutum yake, haka wurin zaman wanda bai san Allah ba yake.”

Ayuba — Chapters