[1] “Wannan ya sa gabana ya fāɗi, zuciyata ta yi tsalle.
[2] Ka saurara! Ka saurari rurin muryarsa, tsawar da take fita daga bakinsa.
[3] Ya saki walƙiyarsa, a ƙarƙashin dukan sammai ya kuma aika ta ko’ina a cikin duniya.
[4] Bayan wannan sai ƙarar rurinsa ta biyo; Ya tsawata da muryarsa mai girma. Sa’ad da ya sāke yin tsawa ba ya rage wani abu.
[5] Muryar Allah tana tsawatawa a hanyoyi masu ban al’ajabi; yana yin manyan abubuwa waɗanda sun wuce ganewarmu.
[6] Yakan ce wa dusar ƙanƙara, ‘Fāɗo a kan duniya,’ ya kuma ce wa ruwa, ‘Zubo da ƙarfi.’
[7] Domin dukan mutanen da ya halitta za su san aikinsa, ya hana kowane mutum yin wahalar aiki.
[8] Dabbobi sun ɓoye; sun zauna cikin kogunansu.
[9] Guguwa tana fitowa daga inda take, sanyi kuma daga iska mai sanyi.
[10] Da numfashinsa Allah yana samar da ƙanƙara sai manyan ruwaye su zama ƙanƙara.
[11] Yana cika gizagizai da lema; yana baza walƙiyarsa ta cikinsu.
[12] Bisa ga bishewarsa suke juyawa a kan fuskar duniya, suna yin dukan abin da ya umarce su su yi.
[13] Yana aiko da ruwa domin horon mutane, ko kuma don yă jiƙa duniya yă kuma nuna ƙaunarsa.
[14] “Ka saurari wannan Ayuba; ka tsaya ka dubi abubuwan al’ajabi na Allah.
[15] Ko ka san yadda Allah yake iko da gizagizai ya kuma sa walƙiyarsa ta haskaka?
[16] Ko ka san yadda gizagizai suke tsayawa cik a sararin sama, waɗannan abubuwa al’ajabi na mai cikakken sani.
[17] Kai mai sa kaya don ka ji ɗumi lokacin da iska mai sanyi take hurawa,
[18] ko za ka iya shimfiɗa sararin sama tare da shi da ƙarfi kamar madubi?
[19] “Gaya mana abin da ya kamata mu ce masa; ba za mu iya kawo ƙara ba domin duhunmu.
[20] Ko za a gaya masa cewa ina so in yi magana? Ko wani zai nemi a haɗiye shi?
[21] Yanzu ba wanda zai iya kallon rana, yadda take da haske a sararin sama bayan iska ta share ta.
[22] Yana fitowa daga arewa da haske na zinariya, Allah yana zuwa da ɗaukaka mai ban al’ajabi.
[23] Maɗaukaki ya fi ƙarfin ganewarmu, shi babban mai iko ne, mai gaskiya da babban adalci, ba ya cutar mutum.
[24] Saboda haka, mutane suke girmama shi, ko bai kula da waɗanda suke gani su masu hikima ba ne?”