Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 0:59

[1] Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa,

[2] “Mulki na Allah ne, dole a ji tsoronsa; yana tafiyar da kome yadda ya kamata a cikin sama.

[3] Za a iya ƙirga rundunarsa? A kan wane ne ba ya haska haskensa?

[4] Ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah? Ta yaya mutumin da mace ta haifa zai zama mai tsarki?

[5] In har wata da taurari ba su da tsarki a idanunsa,

[6] mutum fa? Ai, wannan tsutsa ne, ɗan ƙwaro kawai. Me mutum ya daɗa a gaban Allah!”

Ayuba — Chapters