Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 6:36

[1] “Na yi alkawari da idanuna kada su dubi budurwa da muguwar sha’awa.

[2] Gama mene ne rabon mutum daga Allah a sama, gādonsa daga Maɗaukaki a sama?

[3] Ba masifa ba ne domin mugaye, hallaka kuma ga waɗanda suka yi ba daidai ba?

[4] Bai ga hanyoyina ba ne bai ƙirga kowace takawata ba?

[5] “In da na yi tafiya cikin rashin gaskiya ko kuma ƙafata ta yi sauri zuwa yin ƙarya,

[6] Bari Allah yă auna a kan ma’auni na gaskiya zai kuma san cewa ni marar laifi ne.

[7] In takawata ta kauce daga hanya, in zuciyata ta bi abin da idanuna ke so, ko kuma in hannuwana suna da laifi;

[8] bari waɗansu su ci abin da na shuka, kuma bari a tuge amfanin gonata.

[9] “In sha’awar mace ya shiga mini zuciya, ko kuma na laɓe a ƙofar maƙwabcina,

[10] sai matata ta niƙa hatsin wani kuma waɗansu maza su kwana da ita.

[11] Gama wannan zai zama abin kunya, zunubin da za a yi shari’a a kai.

[12] Wuta ce take ƙuna har ta hallakar; za tă cinye saiwar abin da na shuka ƙurmus.

[13] “In da na danne wa bayina maza da mata hakkinsu, sa’ad da suke da damuwa da ni,

[14] me zan yi lokacin da Allah ya tuhume ni? Me zan ce lokacin da ya tambaye ni?

[15] Shi wanda ya yi ni a cikin uwata ba shi ne ya yi su ba? Ba shi ne ya yi mu a cikin uwayenmu ba?

[16] “In na hana wa matalauta abin da suke so, ko kuma in sa idanun gwauruwa su yi nauyi don kuka,

[17] in na ajiye burodina don kaina kaɗai, ban kuwa ba wa marayu abinci sa’ad da suke jin yunwa,

[18] amma tun suna tasowa na lura da su, kamar yadda mahaifi zai lura da ɗa, kuma tun da aka haife ni ina lura da gwauruwa.

[19] In da na ga wani yana mutuwa don rashin sutura, ko wani mai bukata da ba shi da riga,

[20] kuma zuciyarsa ba tă gode mini ba don na yi masa sutura da gashin tumakina,

[21] in na ɗaga hannuna don in cuci maraya, domin na san in na faɗa za a ji ni a wurin masu shari’a,

[22] bari hannuna yă guntule daga kafaɗata, bari yă tsinke daga inda aka haɗa shi.

[23] Gama ina jin tsoron hallaka daga Allah, kuma domin tsoron ɗaukakarsa ba zan iya yin waɗannan abubuwa ba.

[24] “In na dogara ga zinariya ko kuma na ce wa zallan zinariya, ‘Gare ki nake dogara,’

[25] in na yi fahariya don yawan dukiyata, arzikin da hannuwana suka samu.

[26] In na dubi rana cikin haskenta, ko kuma wata yana tafiyarsa,

[27] zuciyata ta jarrabtu gare su a ɓoye, hannuna kuma ya sumbace su.

[28] Waɗannan ma za su zama zunubin da za a shari’anta ke nan don zai zama na yi wa Allah na sama rashin aminci.

[29] “In na yi murna domin mugun abu ya faru da maƙiyina; ko kuma domin wahala ta same shi,

[30] ban bar bakina yă yi zunubi ta wurin la’anta shi ba,

[31] in mutanen gidana ba su taɓa cewa, ‘Wane ne bai ƙoshi da naman Ayuba ba?’

[32] Ba baƙon da ya taɓa kwana a titi, gama koyaushe ƙofata tana buɗe domin matafiya,

[33] in na ɓoye zunubina yadda mutane suke yi, ta wurin ɓoye laifina a cikin zuciyata,

[34] domin ina tsoron taron mutane kuma ina tsoron wulaƙancin da dangina za su yi mini, sai na yi shiru kuma ban fita waje ba.

[35] (“Kash, da ina da wanda zai ji ni! Na sa hannu ga abin da na faɗa don kāre kaina, bari Maɗaukaki yă amsa mini; bari mai tuhumata da laifi yă yi ƙarata a rubuce.

[36] Ba shakka sai in ɗora a kafaɗata, zan aza a kaina kamar rawani.

[37] Zan ba shi lissafin duk abin da na taɓa yi; zan zo gabansa kamar ɗan sarki.)

[38] “In ƙasata tana kuka da ni kunyoyinta duk sun cika da hawaye,

[39] in na kwashe amfaninta ban biya ba ko kuma na kashe masu ita,

[40] bari ƙaya ta fito a maimakon alkama ciyawa kuma a maimakon sha’ir.” Maganar Ayuba ta ƙare.

Ayuba — Chapters