[1] “Ka san lokacin da awakin kan dutse suke haihuwa? Ko ka taɓa lura da yadda batsiya take haihuwa?
[2] Kana ƙirga watanni nawa suke yi kafin su haihu? Ka san lokacin da suke haihuwa?
[3] Suna kwanciya su haifi ’ya’yansu; naƙudarsu ta ƙare bayan sun haihu.
[4] ’Ya’yansu suna girma kuma suna girma cikin ƙarfi a jeji; sukan tafi ba su dawowa.
[5] “Wane ne yake sakin jakin dawa yă bar shi? Wane ne yake kunce igiyoyinsu?
[6] Na sa jeji yă zama gidansa ƙasar gishiri kuma ta zama wurin zamansa.
[7] Yana dariyar hargitsin da yake faruwa a cikin gari; ba ya jin tsawar mai tuƙa shi.
[8] Yana kiwo a kan tuddai don abincinsa yana neman kowane ɗanyen abu mai ruwan ciyawa.
[9] “Ko ɓauna zai yarda yă zauna a wurin sa wa dabbobi abinci? Zai tsaya a ɗakin dabbobinka da dare?
[10] Ko za ka iya daure shi da igiya a kwarin kunya? Zai yi maka buɗar gonarka?
[11] Ko za ka dogara da shi don yawan ƙarfinsa? Za ka bar masa nauyin aikinka?
[12] Ko za ka amince da shi yă kawo maka hatsinka gida yă tattara shi a masussuka?
[13] “Fikafikan jimina suna bugawa cike da farin ciki amma ba za su gwada kansu da fikafikan da na shamuwa ba.
[14] Tana sa ƙwai nata a ƙasa kuma ta bar su su yi ɗumi a cikin ƙasa,
[15] ba tă damu ko za a taka su a fasa su, ko waɗansu manyan dabbobi za su tattake su.
[16] Tana tsananta wa ’ya’yanta kamar ba nata ba ba tă damu da wahalar da ta sha ba.
[17] Gama Allah bai ba ta hikima ba ko kuma iya fahimta.
[18] Duk da haka sa’ad da ta buɗe fikafikanta ta shara da gudu tana yi wa doki da mai hawansa dariya.
[19] “Ko kai ne kake ba doki ƙarfinsa kai kake rufe wuyansa da geza mai yawa?
[20] Ko kai kake sa shi yă yi tsalle kamar fāra, ba ya jin tsoro sai dai a ji tsoronsa.
[21] Yana takawa da ƙarfi yana jin daɗin ƙarfinsa yana shiga filin yaƙi gabagadi.
[22] Yana yi wa tsoro dariya ba ya jin tsoron kome; ba ya guje wa takobi.
[23] Kwari a baka yana lilo a gabansa kibiya da māshi suna wuce kansa.
[24] Yana kartar ƙasa da ƙarfi; ba ya iya tsayawa tsab sa’ad da ya ji busar ƙaho.
[25] Da jin ƙarar ƙaho sai ya ce, ‘Yauwa!’ Ya ji ƙanshin yaƙi daga nesa, da ihun shugabannin yaƙi.
[26] “Ko ta wurin hikimarka ce shirwa take firiya take kuma baza fikafikanta zuwa kudu?
[27] Ko da umarninka ne shaho yake firiya ya kuma yi sheƙarsa a can sama?
[28] Yana zama a kan dutse yă zauna a wurin da dare; cikin duwatsu ne wurin zamansa.
[29] Daga can yake neman abincinsa; idanunsa suna gani daga nesa.
[30] ’Ya’yansa suna shan jini, inda akwai waɗanda aka kashe nan za a same shi.”