Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 5:03

[1] Sai Ayuba ya amsa,

[2] “Ku saurare ni da kyau; bari wannan yă zama ta’aziyyar da za ku ba ni.

[3] Ku ba ni zarafi in yi magana, bayan na gama sai ku yi ba’arku.

[4] “A wurin mutum ne na kawo kukana? Don me ba zan kāsa haƙuri ba?

[5] Ku dube ni, ku kuma yi mamaki; ku rufe bakina da hannunku.

[6] Lokacin da na yi tunanin wannan, sai in ji tsoro; jikina yă fara rawa.

[7] Don me mugaye suke rayuwa har su tsufa, suna kuma ƙaruwa da iko?

[8] Suna ganin ’ya’yansu suna girma, suna ganin jikokinsu suna tasowa a kan idanunsu.

[9] Gidajensu suna zama cikin lafiya ba ruwansu da fargaba. Kuma Allah ba ya ba su horo.

[10] Shanunsu ba sa fasa haihuwa; suna haihuwa ba sa yin ɓari.

[11] Suna aika ’ya’yansu kamar garke; ’ya’yansu suna guje-guje da tsalle-tsalle.

[12] Suna rera da kayan kiɗa na ganga da garaya; suna jin daɗin busar sarewa.

[13] Suna yin rayuwarsu cikin arziki kuma su mutu cikin salama.

[14] Duk da haka suna ce wa Allah, ‘Ka rabu da mu.’ Ba ma so mu san hanyoyinka.

[15] Wane ne Maɗaukaki har da za mu bauta masa? Wace riba za mu samu ta wurin yin addu’a gare shi?

[16] Amma arzikinsu ba a hannunsu yake ba saboda haka ba ruwana da shawarar mugaye.

[17] “Duk da haka, sau nawa fitilar mugu take mutuwa? Sau nawa bala’i yake auka masa, ko Allah ya taɓa hukunta mugu cikin fushi?

[18] Sau nawa suke zama kamar tattaka a iska, ko kuma kamar ƙura da iskar hadari take kwashewa?

[19] An ce ‘Allah yana tara wa ’ya’yan mutum horon da zai ba mutumin.’ Bari yă ba mutumin horo don yă san ya yi haka!

[20] Bari idanunsa su ga yadda zai hallaka; bari yă sha daga fushin Maɗaukaki.

[21] Ko zai damu da iyalin da ya bari a baya sa’ad da kwanakinsa suka ƙare?

[22] “Wani zai iya koya wa Allah ilimi tun da yana shari’anta har da waɗanda suke manya masu iko?

[23] Wani mutum zai mutu cikin jin daɗi da kwanciyar hankali,

[24] jikinsa ɓulɓul, ƙasusuwansa da alamar ƙarfi.

[25] Wani kuma zai mutu cikin ɗacin rai, bai taɓa jin daɗin wani abu mai kyau ba.

[26] Dukansu kuwa za a bizne su a ƙasa, kuma tsutsotsi za su cinye su.

[27] “Na san duk abin da kuke tunani, yadda za ku saɓa mini.

[28] Kuna cewa, ‘Yanzu ina gidan babban mutumin nan, tenti wurin da mugaye suke zama?’

[29] Ba ku taɓa tambayar waɗanda suke tafiya ba? Ba ku kula da labaransu,

[30] cewa an kāre mugu daga ranar bala’i, an kāre shi daga ranar fushi?

[31] Wane ne yake gaya masa abin da ya yi? Wane ne yake rama abin da ya yi?

[32] Za a bizne shi a kabari, a kuma yi tsaron kabarinsa.

[33] Akan mai da ƙasa a kan gawarsa a hankali; dukan jama’a suna binsa, da yawa kuma suna gabansa.

[34] “Saboda haka ta yaya za ku iya yi mini ta’aziyya da surutan banzan nan naku? Babu wani abu cikin amsarku sai ƙarya!”

Ayuba — Chapters