Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:21

[1] Sai Ayuba ya amsa,

[2] “Na ji abubuwa da yawa kamar waɗannan; dukanku ba ku iya ta’aziyya ba!

[3] Dogayen surutanku ba sa ƙare ne? Me yake sa kuke ta yin waɗannan surutai har kuke cin gaba da yin gardama?

[4] Ni ma zan iya yin maganganu kamar yadda kuke yi in da kuna cikin halin da nake; zan iya faɗar duk abubuwan da kuke faɗi, in kaɗa muku kaina.

[5] Amma bakina zai ƙarfafa ku; ta’aziyyar da za tă fito daga bakina za tă kawar muku da ɓacin zuciyarku.

[6] “Duk da haka in na yi magana, ba na samun sauƙi; in ma na yi shiru zafin ba ya tafiya.

[7] Ba shakka ya Allah ka gajiyar da ni; ka ɓata gidana gaba ɗaya.

[8] Ka daure ni, ya kuma zama shaida; yadda na rame sai ƙasusuwa, wannan ya sa ake gani kamar don ni mai zunubi ne shi ya sa.

[9] Allah ya kai mini hari ya yi kaca-kaca da ni cikin fushinsa yana cizon haƙoransa don fushin da yake yi da ni; ya zura mini ido.

[10] Mutane suka buɗe baki suka yi mini riyar reni; suka yi mini ba’a suka haɗu suka tayar mini.

[11] Allah ya bashe ni ga mugayen mutane, ya jefa ni hannun mugaye.

[12] Dā ina zamana lafiya kome yana tafiya daidai; amma ya ragargaza ni; ya shaƙe ni a wuya; ya murƙushe ni na zama abin barata gare shi;

[13] maharbansa sun kewaye ni. Ba tausayi, ya soke ni a ƙodata har jini ya zuba a ƙasa.

[14] Ya ji mini rauni a kai a kai ya auko mini kamar mai yaƙi.

[15] “Ina makoki saye da tsummoki na ɓoye fuskata a cikin ƙura.

[16] Fuskata ta yi ja don kuka idanuna sun kukumbura;

[17] duk da haka hannuwana ba su aikata ɓarna ba kuma addu’ata mai tsabta ce.

[18] “Ya duniya, kada ki ɓoye jinina; bari yă yi kuka a madadina!

[19] Ko yanzu haka shaidata tana sama; wanda zai tsaya mini yana sama.

[20] Shi mai yin roƙo a madadina abokina ne yayinda nake kuka ga Allah;

[21] a madadin mutum ya yi roƙo ga Allah kamar yadda mutum yakan yi roƙo domin abokinsa.

[22] “Shekaru kaɗan suka rage in kama hanyar da ba a komawa.

Ayuba — Chapters