Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 2:31

[1] Sa’an nan Ayuba ya amsa,

[2] “Ko a yau, ina kuka mai zafi; hannunsa yana da nauyi duk da nishin da nake yi.

[3] Da a ce na san inda zan same shi; da a ce zan iya zuwa wurin da yake zama!

[4] Zan kai damuwata wurinsa in yi gardama da shi.

[5] Zan nemi in san abin da zai ce mini, in kuma auna abin da zai ce mini.

[6] Zai yi gardama da ni da ikonsa mai girma? Babu, ba zai zarge ni da laifi ba.

[7] Mai adalci ne zai kawo ƙara a wurinsa, kuma zan samu kuɓuta daga wurin mai shari’an nan har abada.

[8] “Amma in na je gabas, ba ya wurin; in na je yamma, ba zan same shi ba.

[9] Sa’ad da yake aiki a arewa, ba ni ganinsa; sa’ad da ya juya zuwa kudu, ba na ganinsa.

[10] Amma ya san hanyar da nake bi; sa’ad da ya gwada ni zan fito kamar zinariya.

[11] Ƙafafuna suna bin ƙafafunsa kurkusa; na bi hanyarsa ba tare da na juya ba.

[12] Ban fasa bin dokokin da ya bayar ba; na riƙe maganarsa da muhimmanci fiye da abincin yau da gobe.

[13] “Amma ya tsaya shi kaɗai, kuma wa ya isa yă ja da shi? Yana yin abin da yake so.

[14] Yana yi mini abin da ya shirya yă yi mini, kuma yana da sauran irinsu a ajiye.

[15] Shi ya sa na tsorata a gabansa; sa’ad da na yi tunanin wannan duka, nakan ji tsoronsa.

[16] Allah ya sa zuciyata ta yi sanyi; Maɗaukaki ya tsorata ni.

[17] Duk da haka duhun bai sa in yi shiru ba, duhun da ya rufe mini fuska.

Ayuba — Chapters