Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:25

[1] “Na gaji da rayuwa; saboda haka bari in faɗi zuciyata gabagadi yadda raina yake jin ba daɗi.

[2] Zan ce wa Allah, kada ka hukunta ni, amma ka gaya mini laifin da na yi maka.

[3] Kana jin daɗin ba ni wahala, don me ka yashe ni, abin da ka halitta da hannunka, yayinda kake murmushi game da shirye-shiryen mugaye?

[4] Idanunka irin na mutum ne? Kana gani yadda mutum yake gani ne?

[5] Kwanakinka kamar na mutane ne, ko shekarunka kamar na mutane ne

[6] da za ka neme ni da laifi ka hukunta ni?

[7] Ko da yake ka san ba ni da laifi, kuma ba wanda zai iya cetona daga hannunka.

[8] “Da hannuwanka ka ƙera ni, kai ka halicce ni. Yanzu kuma kai za ka juya ka hallaka ni?

[9] Ka tuna cewa ka mulmula ni kamar yumɓu. Yanzu za ka mai da ni in zama ƙura kuma?

[10] Ba kai ka zuba ni kamar madara ba, na daskare kamar cuku.

[11] Ka rufe ni da tsoka da fata, ka harhaɗa ni da ƙasusuwa da jijiyoyi?

[12] Ka ba ni rai ka kuma yi mini alheri, kuma cikin tanadinka ka kula da ruhuna.

[13] “Amma wannan shi ne abin da ka ɓoye a zuciyarka, na kuma san abin da yake cikin zuciyarka ke nan.

[14] In na yi zunubi kana kallo na kuma ba za ka fasa ba ni horo ba don laifin da na yi.

[15] Idan ina da laifi, kaitona! Ko da ba ni da laifi, ba zan iya ɗaga fuskata ba, gama kunya ta ishe ni duk ɓacin rai ya ishe ni.

[16] In na ɗaga kaina, za ka neme ni kamar zaki ka sāke nuna al’ajabin ikonka a kaina.

[17] Kana sāke kawo sababbin waɗanda za su ba da shaida a kaina kana ƙara haushinka a kaina; kana ƙara kawo mini hari.

[18] “Me ya sa ka fito da ni daga cikin uwata? Da ma na mutu kafin a haife ni.

[19] Da ma ba a halicce ni ba, da na mutu tun daga cikin cikin uwata na wuce zuwa kabari!

[20] ’Yan kwanakina ba su kusa ƙarewa ba ne? Ka rabu da ni don in ɗan samu sukuni na ɗan lokaci

[21] kafin in koma inda na fito, ƙasa mai duhu da inuwa sosai,

[22] zuwa ƙasa mai duhun gaske, da inuwa da hargitsi, inda haske yake kamar duhu.”

Ayuba — Chapters