Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:20

[1] Sa’an nan Zofar mutumin Na’ama ya amsa,

[2] “Duk surutun nan ba za a amsa maka ba? Ko mai surutun nan marar laifi ne?

[3] Ko maganganun nan naka marasa amfani za su sa mutane su yi maka shiru? Ba wanda zai kwaɓe ka lokacin da kake faɗar maganar da ba daidai ba?

[4] Ka ce wa Allah, ‘Abin da na gaskata ba laifi ba ne kuma ni mai tsabta ne a gabanka.’

[5] Da ma Allah zai yi magana, yă buɗe baki yă faɗi wani abin da ka yi da ba daidai ba

[6] yă kuma buɗe maka asirin hikima, gama hikima ta gaskiya tana da gefe biyu. Ka san wannan, Allah ya riga ya manta da waɗansu zunubanka.

[7] “Ko za ka iya gane al’amuran Allah? Ko za ka iya gane girman asirin Maɗaukaki?

[8] Sun fi nisan sama tudu, me za ka iya yi? Sun fi zurfin kabari zurfi, me za ka sani?

[9] Tsayinsu ya fi tsawon duniya da kuma fāɗin teku.

[10] “In ya zo ya kulle ka a kurkuku ya ce kai mai laifi ne, wa zai hana shi?

[11] Ba shakka yana iya gane mutanen da suke marasa gaskiya; kuma in ya ga abin da yake mugu, ba ya kula ne?

[12] Amma daƙiƙin mutum ba ya taɓa zama mai hikima kamar dai a ce ba a taɓa haihuwar ɗan aholaki horarre.

[13] “Duk da haka in ka miƙa masa zuciyarka, ka kuma miƙa hannuwanka gare shi,

[14] in ka kawar da zunubin da yake hannunka, ba ka bar zunubi ya kasance tare da kai ba

[15] shi ne za ka iya ɗaga fuskarka ba tare da jin kunya ba; za ka tsaya da ƙarfi kuma ba za ka ji tsoro ba.

[16] Ba shakka za ka manta da wahalolinka, za ka tuna da su kamar yadda ruwa yake wucewa.

[17] Rayuwarka za tă fi hasken rana haske, duhu kuma zai zama kamar safiya.

[18] Za ka zauna lafiya, domin akwai bege; za ka duba kewaye da kai ka huta cikin kwanciyar rai.

[19] Za ka kwanta, ba wanda zai sa ka ji tsoro, da yawa za su zo neman taimako a wurinka.

[20] Amma idanun mugaye ba za su iya gani ba, kuma ba za su iya tserewa ba; begensu zai zama na mutuwa.”

Ayuba — Chapters