[1] “Amma yanzu suna yi mini ba’a waɗanda na girme su, waɗanda iyayensu maza ba su isa su zama karnukan kiwon garken tumakina ba.
[2] Ina amfani ƙarfin hannuwansu gare ni, tun da ba su da sauran kuzari?
[3] Duk sun rame don rashi da yunwa, suna yawo a gaigayar ƙasa a kufai da dare.
[4] A cikin jeji suna tsinkar ganyaye marasa daɗi, jijiyoyin itacen kwakwa ne abincinsu.
[5] An kore su daga cikin mutanensu, aka yi musu ihu kamar ɓarayi.
[6] An sa dole su zauna a kwazazzabai da kuma cikin kogunan duwatsu da kuma cikin ramummuka cikin ƙasa.
[7] Suka yi ta kuka kamar dabbobi a jeji, suka taru a ƙarƙashin sarƙaƙƙiya.
[8] Mutane marasa hankali marasa suna, an kore su daga ƙasar.
[9] “Yanzu kuma ’ya’yansu maza su suke yi mini ba’a cikin waƙa na zama abin banza a gare su.
[10] Suna ƙyamata suna guduna; suna tofa mini miyau a fuska.
[11] Yanzu da Allah ya kunce bakana ya ba ni wahala sun raba ni da mutuncina.
[12] A hannun damana ’yan tā-da-na-zaune-tsaye sun tayar; sun sa tarko a ƙafafuna, sun yi shirin hallaka ni.
[13] Sun ɓata mini hanyata; sun yi nasara cikin hallaka ni, ba tare da wani ya taimake su ba.
[14] Suka nufo ni daga kowane gefe; suka auko mini da dukan ƙarfinsu.
[15] Tsoro ya rufe ni; an kawar mini mutuncina kamar da iska, dukiyata ta watse kamar girgije.
[16] “Yanzu raina yana ƙarewa; kwanakin wahala sun kama ni.
[17] Dare ya huda ƙasusuwana; ina ta shan azaba ba hutawa.
[18] A cikin girman ikonsa Allah ya zama kamar riga a jikina; ya shaƙe ni kamar wuyan rigata.
[19] Ya jefa ni cikin laka, na zama ba kome ba sai ƙura da toka.
[20] “Na yi kuka gare ka ya Allah, amma ba ka amsa mini ba. Na tashi tsaye, amma sai ka dube ni kawai.
[21] Ka dube ni ba tausayi; Ka kai mini hari da ƙarfin hannunka.
[22] Ka ɗaga ni sama ka ɗora ni a kan iska; ka jujjuya ni cikin hadari.
[23] Na san za ka sauko da ni ga mutuwa zuwa wurin da kowane mai rai zai je.
[24] “Ba shakka ba mai ɗora hannu a kan mutumin da yake cikin wahala. Lokacin da ya yi kukan neman taimako a cikin wahalarsa.
[25] Ashe ban yi kuka domin waɗanda suke cikin damuwa ba? Ko zuciyata ba tă yi baƙin ciki domin matalauta ba?
[26] Duk da haka sa’ad da nake begen abu mai kyau, mugun abu ne ya zo; Sa’ad da nake neman haske, sai duhu ya zo.
[27] Zuciyata ba tă daina ƙuna ba; ina fuskantar kwanakin wahala.
[28] Na yi baƙi ƙirin, amma ba rana ce ta ƙona ni ba. Na tsaya a cikin mutane, na kuma yi kuka don taimako.
[29] Na zama ɗan’uwan diloli, na zama abokan mujiyoyi.
[30] Fatar jikina ta yi baƙi tana ɓarewa; jikina yana ƙuna da zazzaɓi.
[31] Garayata ta zama ta makoki, sarewata kuma ta zama ta kuka.