Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 4:50

[1] “Ko za ka iya kama dodon ruwa da ƙugiyar kamar kifi ko kuma ka daure harshenta da igiya?

[2] Za ka iya sa igiya a cikin hancinta ko kuma ka huda muƙamuƙanta da ƙugiya?

[3] Za tă ci gaba da roƙonka ka yi mata jinƙai? Ko za tă yi maka magana a hankali?

[4] Za tă yi yarjejjeniya da kai don ka ɗauke ta tă zama baiwa gare ka dukan kwanakin ranta?

[5] Za ka yi wasa da ita kamar yadda za ka yi da tsuntsu? Ko za ka daure ta da tsirkiya domin bayinka mata?

[6] ’Yan kasuwa za su saye ta ko za su raba ta a tsakaninsu?

[7] Ko za ka iya huda fatarta da kibiya ka kuma huda kansa da māsu?

[8] In ka ɗora hannunka sau ɗaya a kanta za ka tuna da yaƙin da ba za ka sāke yi ba!

[9] Duk ƙoƙarin kama ta banza ne; ganin ta kawai abin tsoro ne.

[10] Ba wanda ya isa yă tsokane ta. Wane ne kuma ya isa yă yi tsayayya da ni?

[11] Wane ne yake bi na bashi da dole in biya? Duk abin da yake ƙarƙashin sama nawa ne.

[12] “Ba zan daina magana game da gaɓoɓinta ba ƙarfinta da kuma kyan kamanninta ba.

[13] Wa zai iya tuɓe mata mayafinta? Wa zai iya shiga tsakanin ɓawonta.

[14] Wa zai iya buɗe ƙofofin bakinta? Haƙoranta ma abin tsoro ne?

[15] An rufe bayanta da jerin garkuwoyi aka manne su sosai.

[16] Suna kurkusa da juna yadda da ƙyar iska take iya wucewa tsakani.

[17] An haɗa su da juna sun mannu da juna kuma ba za a iya raba su ba.

[18] Numfashinta yana fitar da wuta; idanunta kamar hasken zuwan safe.

[19] Wuta tana fitowa daga bakinta; tartsatsin wuta suna fitowa,

[20] Hayaƙi yana fitowa daga hancinta kamar daga tukunya mai tafasa a kan wutar itace.

[21] Numfashinta yana sa garwashi yă kama wuta, harshen wuta yana fita daga bakinta.

[22] Akwai ƙarfi a cikin wuyanta; razana tana wucewa a gabanta.

[23] Namanta yana da kauri a manne da juna; naman yana da tauri ba ya matsawa.

[24] Ƙirjinta yana da ƙarfi kamar dutse, da ƙarfi kamar dutsen niƙa.

[25] Sa’ad da ta tashi, manya suna tsorata; suna ja da baya.

[26] Takobi ba ta iya yankanta, kibiya ko māshi ba sa iya huda ta.

[27] Ƙarfe kamar kara ne a wurinta tagulla kuma kamar ruɓaɓɓen katako ne a wurinta.

[28] Māsu ba su sa ta tă gudu; jifar majajjawa kamar na ciyawa ne gare ta.

[29] Kulki a gare ta kamar ciyawa ne, tana dariyar wucewar māshi.

[30] Cikinta yana rufe a ɓawo masu ƙarfi, tana kabtar ƙasa in tana tafiya.

[31] Tana sa zurfin kogi yă tafasa kamar tukunya, ta kuma sa teku yă zama kamar tukunyar man shafawa.

[32] A bayanta ya bar haske kamar zurfin ruwan da yana kumfa.

[33] Ba wani abu kamar ta a duniya, halitta marar tsoro.

[34] Tana rena duk masu girman kai. Ita take mulki kan duk masu girman kai.”

Ayuba — Chapters