Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:55

[1] Bayan wannan Ayuba ya buɗe baki ya la’anta ranar da aka haife shi.

[2] Ayuba ya ce,

[3] “A hallaka ranar da aka haife ni, da kuma daren da aka ce, ‘An haifi jariri namiji!’

[4] Bari ranan nan ta zama duhu; kada Allah yă kula da ita; kada rana tă yi haske a wannan rana.

[5] Bari duhu da inuwa mai duhu ta sāke rufe ta; gizagizai kuma su rufe ta; duhu kuma ya rufe haskenta.

[6] Bari duhu mai yawa yă rufe daren nan; kada a haɗa ta cikin kwanakin shekara, ko kuma cikin kwanakin watanni.

[7] Bari daren yă zama marar amfani; kada a ji wata sowa ta farin ciki.

[8] Bari waɗanda suke la’anta ranaku su la’anta wannan rana su waɗanda suke umartar dodon ruwa.

[9] Bari taurarinta na safe su zama duhu; bari ranar tă yi ta jiran ganin haske amma kada tă gani,

[10] gama ba tă hana uwata ɗaukar cikina, don ta hana ni shan wahalan nan ba.

[11] “Me ya sa ban mutu ba da za a haife ni, ko kuma in mutu sa’ad da ana haihuwata ba?

[12] Me ya sa aka haife ni, aka tanada nono na sha na rayu?

[13] Da yanzu ina kwance cikin salama; da ina barcina cikin salama

[14] tare da sarakuna da mashawarta a cikin ƙasa, waɗanda suka gina wa kansu wuraren da yanzu duk sun rushe,

[15] da shugabanni waɗanda suke da zinariya, waɗanda suka cika gidajensu da azurfa.

[16] Ko kuma don me ba a ɓoye ni a cikin ƙasa kamar jaririn da aka haifa ba rai ba, kamar jaririn da bai taɓa ganin hasken rana ba.

[17] A wurin mugaye za su daina yin mugunta, gajiyayyu kuma za su huta.

[18] Waɗanda aka daure za su sami jin daɗin; an sake su ba za su sāke jin ana tsawata masu ba.

[19] Manyan da ƙanana suna a can, bawa kuma ya sami ’yanci daga wurin maigidansa.

[20] “Don me ake ba da haske ga waɗanda suke cikin ƙunci, rai kuma ga masu ɗacin rai

[21] ga waɗanda suke neman mutuwa amma ba su samu ba, waɗanda suke nemanta kamar wani abu mai daraja a ɓoye,

[22] waɗanda suke farin ciki sa’ad da suka kai kabari?

[23] Don me aka ba mutum rai, mutumin da bai san wani abu game da kansa ba, mutumin da Allah ya kange shi.

[24] Baƙin ciki ya ishe ni maimakon abinci; ina ta yin nishi ba fasawa;

[25] Abin da nake tsoro ya faru da ni; abin da ba na so ya same ni.

[26] Ba ni da salama, ba natsuwa; ba ni da hutu, sai wahala kawai.”

Ayuba — Chapters