Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:20

[1] Sai Elifaz mutumin Teman ya amsa,

[2] “In wani ya yi maka magana, za ka ji haushi? Amma wa zai iya yin shiru?

[3] Ka tuna yadda ka yi wa mutane da yawa magana, yadda ka ƙarfafa hannuwa marasa ƙarfi.

[4] Maganarka ta ƙarfafa waɗanda suka yi tuntuɓe; ka ƙarfafa gwiwoyin da suka rasa ƙarfinsu.

[5] Amma yanzu wahala ta zo maka, sai ka karaya; wahala ta sa ka rikice.

[6] Ashe bai kamata ka dogara ga Allahnka ba, amincinka kuma yă zama begenka?

[7] “Ka duba ka gani yanzu. Wane marar laifi ne ya taɓa hallaka? Ko an taɓa hallaka masu adalci?

[8] Na kula cewa waɗanda suke huɗa gonar mugunta, da waɗanda suke shuka mugunta, su ne suke girbe mugunta.

[9] A sa’a ɗaya Allah yake hallaka su, cikin fushinsa yakan hallaka su.

[10] Zakoki suna ruri suna gurnani; duk da haka an karya haƙoran manyan zakoki.

[11] Zakoki suna mutuwa domin ba dabbar da za su kashe su ci, ’ya’yan zakanya kuma sun watse.

[12] “Asirce aka gaya mini maganan nan, da ƙyar kunnuwana suka iya ji.

[13] Cikin mafarki da tsakar dare, lokacin kowa yana zurfin barci, na sami saƙon nan.

[14] Tsoro da fargaba suka kama ni har duk ƙasusuwan jikina suka yi ta rawa.

[15] Wani iska ya taɓa mini fuska, sai tsigar jikina ta tashi.

[16] Ya tsaya cik, amma ban iya sani ko mene ne ba. Wani abu ya tsaya a gabana, na kuma ji murya.

[17] ‘Ko zai yiwu mutum yă fi Allah adalci, ko kuma mutum yă fi wanda ya halicce shi tsarki?

[18] In Allah bai yarda da bayinsa ba, in ya sami mala’ikunsa da laifi,

[19] to, su wane ne mutane masu zama a gidan da aka yi da laka, waɗanda da ƙura aka yi harsashensu, waɗanda za a iya murƙushe su kamar asu!

[20] Tsakanin safe da yamma mai yiwuwa ne ragargaza su; farat ɗaya, su mutu har abada.

[21] Ba a tuge igiyar tentinsu, don su mutu ba tare da hikima ba?’

Ayuba — Chapters