[1] Sai Ayuba ya amsa,
[2] “Yadda ka taimaki marar ƙarfi! Yadda ka ceci marar ƙarfi!
[3] Ka ba marar hikima shawara! Ka nuna kana da ilimi sosai.
[4] Wane ne ya taimake ka ka yi waɗannan maganganu? Kuma ruhun wane ne ya yi magana ta bakinka?
[5] “Matattu suna cikin azaba, waɗanda suke ƙarƙashin ruwaye da dukan mazauna cikin ruwaye.
[6] Mutuwa tsirara take a gaban Allah; haka kuma hallaka take a buɗe.
[7] Ya shimfiɗa arewancin sararin sama a sarari; ya rataye duniya ba a jikin wani abu ba.
[8] Ya naɗe ruwaye a cikin gizagizansa, duk da haka girgijen bai yage saboda nauyi ba.
[9] Ya rufe fuskar wata, ya shimfiɗa gizagizai a kan shi,
[10] ya zāna iyakar fuskar ruwa a kan iyakar da take tsakanin duhu da haske.
[11] Madogaran sama sun girgiza, saboda tsawatawarsa.
[12] Da ikonsa ya kwantar da teku; da hikimarsa ya hallaka dodon ruwan nan Rahab.
[13] Da numfashinsa ya sa sararin sama ya yi kyau da hannunsa ya soke macijin nan mai gudu.
[14] Waɗannan kaɗan ke nan daga cikin ayyukansa masu yawa. Kaɗan kawai muke ji game da shi! Wane ne kuwa yake iya gane tsawar ikonsa?”