Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:35

[1] “Mutum bai sha wahalar aiki ba a duniya? Rayuwarsa ba kamar ta wanda aka yi hayarsa ba ne?

[2] Kamar yadda bawa yakan jira yamma ta yi, ko kuma kamar yadda wanda aka yi hayarsa yakan jira a biya shi kuɗin aikin da ya yi.

[3] Saboda haka rabona shi ne watanni na zama banza, kowane dare kuwa sai ɓacin rai nake samu.

[4] Lokacin da na kwanta ina tunani, ‘Har sai yaushe zan tashi?’ Gari ya ƙi wayewa, ina ta jujjuyawa har safe.

[5] Jikina duk tsutsotsi da ƙuraje sun rufe shi, fatar jikina ta ruɓe tana fitar da ruwan miki.

[6] “Kwanakina suna wucewa da sauri, fiye da yadda ƙoshiyar masaƙa take wucewa da sauri, za su kawo ga ƙarshe ba bege.

[7] Ka tuna, ya Allah, raina numfashi ne kawai; idanuna ba za su taɓa sāke ganin farin ciki ba.

[8] Idanun da suke ganina yanzu ba za su sāke ganina ba; za ku neme ni amma ba za ku same ni ba.

[9] Kamar yadda girgije yakan ɓace yă tafi, haka mutum yake shige zuwa kabari ba kuwa zai dawo ba.

[10] Ba zai taɓa zuwa gidansa ba; ba za a sāke san da shi ba.

[11] “Saboda haka ba zan yi shiru ba; zan yi magana cikin ɓacin raina, zan nuna ɓacin raina cikin ruhu, cikin ƙuncin raina.

[12] Ni teku ne, ko kuwa dodon ruwa, don me kake tsaro na?

[13] Lokacin da nake zato zan sami salama in na kwanta a gadona don in huta,

[14] duk da haka kana ba ni tsoro da mafarke-mafarke, kana tsorata ni da wahayi.

[15] Na gwammace a shaƙe ni in mutu maimakon in kasance cikin wannan jiki.

[16] Ba na so in zauna da rai; ba zan rayu ba har abada. Ku rabu da ni; rayuwata ba ta da amfani.

[17] “Mene ne mutum har da ka kula da shi haka, har ka mai da hankali a kansa,

[18] har kake duba shi kowace safiya, kake kuma gwada shi koyaushe?

[19] Ba za ka ɗan daina kallo na ba ko ka rabu da ni na ɗan lokaci?

[20] In na yi zunubi, me na yi maka, kai mai lura da mutane? Don me ka sa ni a gaba? Na zame maka kaya mai nauyi ne?

[21] Me ya sa ba za ka gafarta mini laifofina ba? Gama na kusa kwantawa cikin ƙasa; za ka neme ni, amma ba za ka same ni ba.”

Ayuba — Chapters