Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 4:23

[1] Akwai ramin azurfa akwai kuma wurin da ake tace zinariya.

[2] Daga cikin ƙasa ake ciro ƙarfe, ana kuma narkar da tagulla daga cikin dutse.

[3] Mutum ya kawo ƙarshen duhu; yakan bincike zuzzurfar iyaka, yana neman duwatsu a wuri mafi duhu.

[4] Nesa da inda mutane suke zama, yakan huda rami yă yi abin lilo, a wurin da mutane ba sa bi.

[5] Cikin ƙasa inda ake samun abinci, a ƙarƙashinta kuwa zafi ne kamar wuta;

[6] akwai duwatsu masu daraja a cikin duwatsunta, akwai kuma zinariya a cikin ƙurarta.

[7] Tsuntsu mai farauta bai san hanyarta ba, ba shahon da ya taɓa ganin ta.

[8] Manyan namun jeji ba su taɓa binta ba, ba zakin da ya taɓa binta.

[9] Hannun mutum ya iya sarrafa ƙanƙarar duwatsu, yă kuma tumɓuke tushen duwatsu.

[10] Yana tona rami a cikin duwatsu idanunsa suna ganin dukan dukiyar da ke cikin duwatsun.

[11] Yana nema daga ina ruwan rafi yake ɓulɓulowa yana kuma binciko abubuwan da suke a ɓoye yă kawo su cikin haske.

[12] Amma a ina ne za a iya samun hikima? Ina fahimta take zama?

[13] Mutum bai gane muhimmancinta ba, ba a samunta a ƙasar masu rai.

[14] Zurfi ya ce, “Ba ta wurina”; teku ya ce, “Ba ta wurina.”

[15] Ba irin zinariyar da za tă iya sayenta, ko kuma a iya auna nauyinta da azurfa.

[16] Ba za a iya sayenta da zinariyar Ofir, ko sauran duwatsu masu daraja ba.

[17] Zinariya da madubi ba za su iya gwada kansu da ita ba, ba kuwa za a iya musayarta da abubuwan da aka yi da zinariya ba.

[18] Kada ma a ce murjani da duwatsu masu walƙiya; farashin hikima ya fi na lu’ulu’ai.

[19] Ba za a iya daidaita darajarta da duwatsun Tofaz na Kush ba, zallar zinariya ma ba tă isa ta saye ta ba.

[20] “To, daga ina ke nan hikima ta fito? Ina fahimta take zama?

[21] An ɓoye ta daga idanun kowane abu mai rai, har tsuntsayen sararin sama ma an ɓoye masu ita.

[22] Hallaka da mutuwa suna cewa, ‘Jita-jitarta kaɗai muke ji.’

[23] Allah ya gane hanyar zuwa wurinta. Shi ne kaɗai ya san inda take zama,

[24] Gama yana ganin iyakar duniya kuma yana ganin duk abin da yake ƙarƙashin sama.

[25] Lokacin da ya yi iska ya sa ta hura, ya kuma auna ruwaye.

[26] Lokacin da ya yi wa ruwan sama doka da kuma hanya domin walƙiya,

[27] sai ya dubi hikima ya auna ta; ya tabbatar da ita, ya gwada ta.

[28] Ya kuma ce wa mutum, ‘Tsoron Ubangiji shi ne hikima, kuma guje wa mugunta shi ne fahimi.’ ”

Ayuba — Chapters