Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 4:58

[1] “Domin me Maɗaukaki ba zai sa ranar shari’a ba? Don me waɗanda suka san shi suke faman samun irin ranakun nan?

[2] Mugaye suna satar fili ta wurin matsar da duwatsun da aka yi iyaka da su; suna satar dabbobi su kuma yi kiwon su.

[3] Suna ƙwace wa marayu jakunansu suna kuma ƙwace wa gwauruwa sa don suna binta bashi.

[4] Suna ture matalauta daga hanya suna kuma sa dole matalautan ƙasar su ɓoye.

[5] Kamar jakunan jeji a hamada, matalauta suna aikin neman abinci gonaki marasa amfani suna tanada abinci wa ’ya’yansu.

[6] Suna girbi a gonakin da ba nasu ba, suna yin kala a gonar inabi ta mugaye.

[7] Don ba su da tufafi, sukan kwana tsirara; ba su da wani abin da zai rufe su cikin sanyi.

[8] Sun jiƙe sharkaf da ruwan da yake kwararowa daga duwatsu, sun rungume duwatsu don rashin wurin fakewa.

[9] Ana ƙwace jinjiri mai shan mama; ana ƙwace ɗan yaron matalauci don biyan bashi.

[10] Don ba su da tufafi suna yawo tsirara; suna dakon dammunan hatsi amma duk da haka suna cikin shan yunwa.

[11] Suna matse zaitun a cikin kunyoyi suna kuma matse ruwan inabi daga ’ya’yan inabi, duk da haka suna fama da ƙishi.

[12] Ana jin nishin masu mutuwa daga birni, kuma rayukan waɗanda aka ji musu rauni suna kuka suna kira don taimako. Amma bai ba wani laifi ba.

[13] “Akwai waɗanda suke yi wa haske tawaye, waɗanda ba su san hanyoyinsa ba ko kuma ba su taɓa bin hanyoyinsa ba.

[14] Sa’ad da hasken yini ya tafi, mai kisankai yakan tashi; yă je yă kashe matalauta da masu bukata; a cikin dare yake shigowa kamar ɓarawo.

[15] Idanun mazinaci suna jiran yamma ta yi sosai; yana tunani cewa, ‘Ba wanda zai gan ni,’ sai kuma yă ɓoye fuskarsa.

[16] Cikin duhu mutane suna fasa gidaje, amma da rana sukan kulle kansu; ba sa so wani abu yă haɗa su da haske.

[17] Gama dukansu, duhu mai yawa shi ne safiyarsu; suna abokantaka da razanar duhu.

[18] “Duk da haka kamar abu marar nauyi suke a kan ruwa; gefen ƙasar da suke, an la’anta ta, yadda ba wanda yake zuwa gonar inabinsu.

[19] Kamar yadda zafi da fări suke shanye ƙanƙarar da ta narke, haka kabari zai ƙwace waɗanda suka yi zunubi.

[20] Waɗanda suka haife su za su manta da su, tsutsotsi za su cinye su; ba za a sāke tunawa da mugaye ba amma an sare su kamar itace.

[21] Suna cutar macen da ba ta da ɗa, suna nuna wa gwauruwa rashin alheri.

[22] Amma Allah cikin ikonsa yakan kawar da masu ƙarfi, ko da yake sun yi ƙarfi, ba su da tabbacin rayuwa.

[23] Mai yiwuwa zai bar su su zauna cikin kwanciyar hankali, amma idanunsa suna kansu.

[24] Sukan samu cin nasara na ɗan lokaci, amma kuma za su ɓace; za su fāɗi a tattara su kamar sauran; za a datse su kamar kan hatsi.

[25] “In wannan ba haka ba ne, wane ne zai shaida ƙarya nake yi har yă ƙi yarda da maganata?”

Ayuba — Chapters