[1] Sai Zofar mutumin Na’ama ya amsa,
[2] “Tunanin da ya dame ni ya sa dole in amsa domin abin ya dame ni sosai.
[3] Na ji wani zargin da ka yi mini na reni, kuma yadda na gane, shi ya sa zan ba da amsa.
[4] “Ba shakka ka san yadda abin yake tuntuni, tun da aka sa mutum cikin duniya,
[5] mugun mutum bai taɓa daɗewa ba, farin cikin mutum na ɗan gajeren lokaci ne.
[6] Ko da ya ƙasaita ya kai sararin sama, kansa kuma yana taɓa gizagizai.
[7] Zai hallaka har abada, kamar bayan gidansa; waɗanda suka gan shi za su ce, ‘Ina yake?’
[8] Kamar mafarki haka zai ɓace, ba za a ƙara ganinsa ba zai ɓace kamar wahayi da dare.
[9] Idon da ya gan shi ba zai ƙara ganinsa ba; wurin zamansa ba zai sāke ganinsa ba.
[10] Dole ’ya’yansa su mayar wa matalauta abin da ya kamata; dole hannuwansa su mayar da dukiyarsa.
[11] Jin ƙarfi da ya cika ƙasusuwansa zai kwantar da shi a cikin ƙura.
[12] “Ko da yake mugunta tana da daɗi a bakinsa kuma yana ɓoye ta a harshensa,
[13] ko da yake ba zai iya rabuwa da ita ba, yana kuma ajiye ta a bakinsa,
[14] duk da haka abincin da ya ci zai zama da tsami a cikin cikinsa; zai zama kamar dafin maciji a cikinsa.
[15] Zai haras da dukiyar da ya haɗiye; Allah zai sa cikinsa yă haras da su.
[16] Zai sha dafin maciji; sarar maciji mai dafi za tă tashe shi.
[17] Ba zai ji daɗin koguna da rafuffuka masu kwarara da zuma da madara ba.
[18] Dole yă ba da abin da ya yi gumi kafin yă samu, ba zai ci ba; ba zai ji daɗin ribar da ya samu daga kasuwancinsa ba.
[19] Gama ya ci zalin talakawa ya bar su cikin wahala; ya ƙwace gidajen da ba shi ya gina ba.
[20] “Ba shakka ba zai samu abin da yake ƙoƙarin samu ba, dukiyarsa ba za tă cece shi ba.
[21] Ba abin da ya ragu da zai ɗauka; arzikinsa ba zai dawwama ba.
[22] Yana cikin samun arziki, ɓacin rai zai auka masa; ƙunci mai ƙarfi zai zo masa.
[23] Lokacin da ya cika cikinsa, Allah zai zuba fushinsa a kansa, zai daddaka shi.
[24] Ko da yake yana guje wa makamin ƙarfe, kibiya mai bakin tagulla za tă huda shi.
[25] Zai zāre ta daga bayansa, tsinin zai fita daga hantarsa; tsoro zai cika shi;
[26] duhu kawai yake jiran dukiyarsa. Wutar da ba a fifita ba za tă cinye shi ta kuma ƙona duk abin da ya rage a tentinsa.
[27] Sammai za su fallasa laifinsa; duniya za tă yi gāba da shi.
[28] Ambaliyar ruwa za tă tafi da gidansa, ruwaye masu gudu a ranar fushin Allah.
[29] Abin da Allah zai sa yă faru da mugu ke nan, gādon da Allah ya ba shi ke nan.”