[1] Maganganun Sarki Lemuwel, magana ce horarriya mahaifiyarsa ta koya masa,
[2] “Ka saurara, ya ɗana! Ka saurara, ɗan cikina! Ka saurara, ya ɗan amshin addu’ata!
[3] Kada ka ba da ƙarfinka a kan mata, ƙarfinka ga waɗanda suka hallaka sarakuna.
[4] “Ba na sarakuna ba ne, ya Lemuwel, ba na sarakuna ba ne su sha ruwan inabi, ba na masu mulki ba ne su yi marmarin barasa,
[5] don kada su sha su manta da abin da doka ta umarta, su hana wa waɗanda aka danne hakkinsu.
[6] A ba da barasa ga waɗanda suke cikin halin ƙaƙa naka yi, ruwan inabi ga waɗanda suke cikin wahala;
[7] bari su sha su manta da talaucinsu kada kuma su ƙara tunawa da ɓacin ransu.
[8] “Yi magana domin bebaye, domin hakkin dukan waɗanda suke naƙasassu.
[9] Yi magana a kuma yi shari’ar adalci; a tsare hakkin talakawa da masu bukata.”
[10] Wa yake iya samun mace mai halin kirki? Darajarta ta fi ta lu’ulu’ai.
[11] Mijinta yana da cikakken amincewa da ita kuma ba ya rasa wani abu mai daraja.
[12] Takan yi masa alheri ba mugunta ba, dukan kwanakin ranta.
[13] Takan zaɓi ulu da lilin ta yi ta saƙa da hannuwanta da farin ciki.
[14] Ita kamar jirgin ’yan kasuwa ne tana kawo abincinta daga nesa.
[15] Takan farka tun da sauran duhu; ta tanada wa iyalinta abinci ta kuma shirya wa ’yan matan gidanta ayyukan da za su yi.
[16] Takan lura da gona sosai ta kuma saye ta; daga abin da take samu na kuɗin shiga take shuka gonar inabi.
[17] Takan himmantu tă yi aikinta tuƙuru; hannuwanta suna da ƙarfi domin ayyukanta.
[18] Takan tabbata akwai riba a kasuwancinta, kuma fitilarta ba ya mutuwa da dare.
[19] Da hannunta take riƙe abin kaɗi ta kuma kama abin saƙa da yatsotsinta.
[20] Takan marabci talakawa takan kuma taimaki masu bukata.
[21] Sa’ad da ƙanƙara ta fāɗi, ba ta jin tsoro saboda gidanta; gama dukansu suna da tufafi masu kauri.
[22] Takan yi wa gadonta kayan shimfiɗa; tufafinta kuma na lilin ne mai laushi na shunayya.
[23] Ana girmama mijinta a ƙofar shiga birni inda yakan zauna a cikin dattawan gari.
[24] Takan yi riguna na lilin ta sayar; takan kuma sayar wa ’yan kasuwa da ɗamara.
[25] Ƙarfi da mutunci su ne suturarta; za tă iya yin dariyar kwanaki masu zuwa.
[26] Tana magana da hikima, kuma umarnai mai aminci yana a harshenta.
[27] Tana lura da sha’anin gidanta kuma ba ta cin abincin ƙyuya.
[28] ’Ya’yanta sukan tashi su ce da ita mai albarka; haka mijinta ma, yakan kuma yabe ta yana cewa,
[29] “Mata da yawa suna yin abubuwan yabo, amma ke kin fi su duka.”
[30] Kayan tsari yana ruɗu, kyau kuma kan shuɗe; amma mace mai tsoron Ubangiji abar yabo ce.
[31] Ka ba ta ladar da ya dace tă samo wa kanta, bari kuma ayyukanta su kawo mata yabo a ƙofar shiga birni.